Yanzu Yanzu: Olu Falae ya bar harkar siyasa kwana daya bayan SDP ta zabi Buhari a matsayin dan takararta

Yanzu Yanzu: Olu Falae ya bar harkar siyasa kwana daya bayan SDP ta zabi Buhari a matsayin dan takararta

- Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Cif Olu Falae ya bar harkar siyasa kwata-kwata

- Falae ya bayyana kalubalen da lafiyarsa ke fuskanta a matsayin dalilinsa na yanke wannan shawara

- Jam'iyyar SDP ne dai ta bayyana Buhari a matsayin dan takararta a zabe mai zuwa

Cif Olu Falae, Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), ya bar harkar siyasa kwata-kwata.

Labarin hukuncinsa na yin ritaya daga harkar siyasa ya bayyana ne a safiyar ranar Juma’a, 8 ga watan Fabrairu.

Yanzu Yanzu: Olu Falae ya bar harkar siyasa kwana daya bayan SDP ta zabi Buhari a matsayin dan takararta

Yanzu Yanzu: Olu Falae ya bar harkar siyasa kwana daya bayan SDP ta zabi Buhari a matsayin dan takararta
Source: Depositphotos

Ya bayyana kalubalen da lafiyarsa ke fuskanta a matsayin dalilinsa na yanke wannan shawara.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Fabrairu ne jam'iyyar ta SDP ta sanar da hukuncinta na marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) baya a zabe mai zuwa.

Jam’iyyar ta bayyana cewa akwai bukatar SDP da APC su hade saboda rikicin da ya billo kai a SDP kan wanda zai yi takarar shugabancin jam’iyyar a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ne suka sanar da hakan bayan wani ganawa da suka yi a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya koka kan wani makirci da ake kullawa na son kama manyan hadimansa

Shugaban SDP na kasa, Cif Olu Falae wanda bai halartan babban taron na iyayen jam’iyyar ba ya samu wakilcin mataimakin Shugaban jam’iyyar na kudu, Farfesa Tunde Adeniran.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa jam’iyyar SDP ta yanke shawarar marawa shugaba Buhari baya ne bayan ta gano cewa ba za ta tabuka abun kirki ba a tseren takarar Shugaban kasa saboda ta rasa lokacin da ya kamata tayi kamfen wajen magance matsalarta na cikin gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel