Zaben Shugaban kasa: Dalilin da yasa SDP ta yi watsi da dan takararta ta dauki Buhari

Zaben Shugaban kasa: Dalilin da yasa SDP ta yi watsi da dan takararta ta dauki Buhari

Jam’iyyar adawa ta Social Democratic Party (SDP) a ranar Alhamis, 7 ga watan Fabrairu ta sanar da hukuncinta na marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) baya a zabe mai zuwa.

Jam’iyyar ta bayyana cewa akwai bukatar SDP da APC su hade saboda rikicin da ya billo kai a SDP kan wanda zai yi takarar shugabancin jam’iyyar a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ne suka sanar da hakan bayan wani ganawa da suka yi a Abuja.

Zaben Shugaban kasa: Dalilin da yasa SDP ta yi watsi da dan takararta ta dauki Buhari

Zaben Shugaban kasa: Dalilin da yasa SDP ta yi watsi da dan takararta ta dauki Buhari
Source: Depositphotos

Shugaban SDP na kasa, Cif Olu Falae wanda bai halartan babban taron na iyayen jam’iyyar ba ya samu wakilcin mataimakin Shugaban jam’iyyar na kudu, Farfesa Tunde Adeniran.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Olu Falae ya bar harkar siyasa kwana daya bayan SDP ta zabi Buhari a matsayin dan takararta

An tattaro cewa dan takara mai neman tikitin Shugaban kasa na jam’iyyar, Farfesa Jerry Gana na kalubalantar dalilin da yasa aka bayyana Mista Donald Duke a matsayin dan takarar Shugaban kasar jam’iyyar bayan shine yayi nasara a zaben fidda gwani da aka gudanar a watan Disamba 2018.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa jam’iyyar SDP ta yanke shwarar marawa shugaba Buhari baya ne bayan ta gano cewa ba za ta tabuka abun kirki ba a tseren takarar Shugaban kasa saboda ta rasa lokacin da ya kamata tayi kamfen wajen magance matsalarta na cikin gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel