Matasa 1,515 ke takarar kujerar majalisar dattawa da na wakilai

Matasa 1,515 ke takarar kujerar majalisar dattawa da na wakilai

Kimanin matasa yan Najeriya 1,515 ne ke neman takarar kujerar majalisar dattawa da majalisar wakilai a zaben kasar mai zuwa.

Mista Ezenwa Nwagwu, mamba a kungiyar YIAGA AFRICA ne ya bayyana hakan a wani taron muhawara kan yan takara matasa a zabe mai zuwa wanda kungiyar ta YIAGA ARICA ta shirya.

Nwagwu yace ya samu adadin ne daga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

“Shigar matasa lamarin siyasa zai basu daman cin moriyan hakkinsu, idan har kundin tsarin mulki ta ba takararsu kariya,” inji shi.

Matasa 1,515 ke takarar kujerar majalisar dattawa da na wakilai

Matasa 1,515 ke takarar kujerar majalisar dattawa da na wakilai
Source: UGC

A cewarsa, adadin ya wakilci kaso 27.4 na majalisar wakilai da kuma kaso 13.5 na majalisar dattawa.

Yace adadin ya zarce aso 18 na majalisar wakilai da kaso 10 na majalisar dattawa da aka samu a sekarar 2015.

KU KARANTA KUMA: EFCC za ta gurfanar da tsohon sakataren gwmnatin tarayya Babachir a ranar Talata

Ya alakata Karin matasa da aka samu ga dokar ba matasa damar shiga a dama dasu a harkar siyasa wanda aka gabatar.

Ya kara da cewa daga cikin yan takarar kujerar sanata 1,904, 253 matasa ne yayinda matasa 1,262 na daga cikin yan takara 4,680 da za su yi takarar majalisar wakilai.

Ms Cynthia Mbamalu, manajan shirin, YIAGA AFRICA tace yan takara kaso 10 ko 14 na yan takarar Shugaban kasa na tsakanin shekaru 35 da 40.

Mbamalu ya bayyana cewa kaso 15 na jam’iyyun siyasa sun cike guraben yan takarar mataimakan Shugaban kasa da mutane yan shekaru 35 da 40.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel