Gwamnatin Najeriya ta waiwayi 'yan Najeriya dake kulle a kasashen waje

Gwamnatin Najeriya ta waiwayi 'yan Najeriya dake kulle a kasashen waje

- Akwai 'yan Najeriya sama da 102 dake gidan yarin kasar chadi

- Najeriya da Chadi dai kasashe ne masu kamanceceniyar al'adu, addinai da yarin

- Kasashen biyu sun sa hannu akan wasu yarjejeniya wadanda ake ganin amfanin su

Gwamnatin Najeriya ta waiwayi 'yan Najeriya dake kulle a kasashen waje

Gwamnatin Najeriya ta waiwayi 'yan Najeriya dake kulle a kasashen waje
Source: UGC

Ofishin jakadancin Najeriya a kasar Chadi a ranar juma'a yace babu kasa da yan Najeriya 102 a gidan yarin kasar dake fuskantar hukuncin laifuka daban daban.

Shugaban ofishin jakadancin Mr Nasiru Waje ya bayyana hakan game wasu manema labarai yan Najeriya da suka kai ziyarar aiki kasar Chadin.

Yace wasu daga cikin yan fursunan da aka yankewa hukunci suna gidajen yari daban daban na kasar.

Waje yace 39 daga cikin yan fursunan sun samu yancin su bayan da ofishin jakadancin suka shiga lamarin.

Yace ana kama yan Najeriya sakamakon laifuka daban daban da suka hada da sumogal da kuma yunkurin amfani da hanya ta cikin chadin da zata sada su da turai.

Shugaban yace mutane 8,000 da suka tsere daga arewa maso kudu saboda Boko Haram suna kasar chadin kuma anyi musu rijista a matsayin yan gudun hijira.

Yace karin mutane 5,000 da rikicin ta'addancin Boko Haram ya ritsa dasu sun samu babban kwamishinan majalisar dinkin duniya yayi musu rijista, kari da cera akwai wasu yan gudun hijiran da basu samu rijista ba daga jihar Yobe.

GA WANNAN: Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

Waje yace Najeriya da Chadi na da dangantaka mai kyau da ta hada rushed daga yare, addini da al'adu masu kamanceceniya.

Ya kara da cewa kasashen suna da yarjejeniya 5 wanda yace sun kara dankon dangantakar su.

Kamar yadda yace akwai:

- Yarjejeniyar hadin kan tsaro.

- Yarjejeniyar cinikayyya.

- Daukaka hannayen jari da tsaron su.

- Darjewa yan kasar zama a dayar kasar ba tare da sun biya ba.

- Yarjejeniyar aiyukan jiragen saman kasashen.

Wadannan yarjejeniyar sun karfafa kasashen biyu ta bangaren tsaro, yaki da ta'addanci da sauransu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel