Atiku ya koka kan wani makirci da ake kullawa na son kama manyan hadimansa

Atiku ya koka kan wani makirci da ake kullawa na son kama manyan hadimansa

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka kan zargin cewa ana kulla wani makirci don kama wasu daga cikin manyan hadimansa a harkokin zabe

- Atiku ya zargi wasu gwamnoni da bai ambaci sunayensu ba daga arewa maso yamma da wani babban minister a wannan gwamnati da aiki tare da All Progressives Congress (APC), don cimma makircinsu

- Kungiyar kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi watsi da rade-radin sannan tayi gargadin cewa adawa ba wani lasisi na aikata laifi bane

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya koka kan zargin cewa ana kulla wani makirci don kama wasu daga cikin manyan hadimansa a harkokin zabe.

Atiku ya zargi wasu gwamnoni da bai ambaci sunayensu ba daga arewa maso yamma da wani babban minista a wannan gwamnati da aiki tare da All Progressives Congress (APC), don cimma makircinsu.

Atiku ya koka kan wani makirci na son kama manyan hadimansa

Atiku ya koka kan wani makirci na son kama manyan hadimansa
Source: UGC

Sai dai kuma kungiyar kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi watsi da rade-radin sannan tayi gargadin cewa adawa ba wani lasisi na aikata laifi bane.

Kakakin kungiyar kamfen din Buhari, Mista Festus Keyamo yace: “Idan basu aikata komai ba toh bai kamata sun ji tsoron komai ba, amma don sun kasance yan adawa ba lasisi bane garesu su aikata abunda ya saba ma doka. Idan suka aikata wani abu ba bisa ka’ida ba yan kwanaki kafin zabe, toh za a kama su.

KU KARANTA KUMA: EFCC za ta gurfanar da tsohon sakataren gwmnatin tarayya Babachir a ranar Talata

Amma a wani jawabi da ya saki a Abuja a jiya, kakakin Atiku, Mista Phrank Shaibu, yace dan takarar Shugaban kasar na PDP yace gwamnatin APC na son kama hadimansa domin kawo cikas ga tsarin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel