Hukumar tsaro ta NSA, tasha alwashin baza ta hana ruwa gudu ba a manyan zabukan makon gobe

Hukumar tsaro ta NSA, tasha alwashin baza ta hana ruwa gudu ba a manyan zabukan makon gobe

- NSA baza su kawo cikas ba a zaben dazai gudana a sati mai zuwa

- Shugaban kasa yayi alkawarin za'a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali

- Kar wani jami'in tsaron daya amince ayi amfani dashi wajen kawo hargitsi a wajen zabe

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Source: Depositphotos

Babban mai bada shawara akan harkar tsaro ta kasa(NSA) Mohammed Monguno ya bawa yan Najeriya tabbacin cewa hukumomin tsaro bazasu kawo cikas ba akan sha'anin zabe.

Mr Monguno tsohon soja mai ritaya ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki wanda hukumar zabe ta INEC ta hada wanda ya gudana a ranar Alhamis a Abuja.

Yace shugaban kasa Muhammad Buhari yace wannan zabe za'a gudanar dashi cikin kwanciyar hankali inda yace zabe ba tashin hankali bane.

"A yayin gudanar da taron kungiyoyin kasa gaba daya kashi na 72 a shekara ta 2017 Buhari ya bada tabbacin gudanar da zaben cikin lumana.

"Inaso na kara bawa masu taraddadi tabbacin cewa hukumomin tsaron bazasu kawo cikas ba.saboda jami'an mutane ne masu amana," cewar Monguno.

GA WANNAN: Masu sanya ido kan zabukan Najeriya na tarayyar Turai sun maida martani kan kalaman Malam Nasir Elrufai

Ya bada tabbacin za'a bawa kowanne dan Najeriya damar sa ta hanyar daya kamata.

"An wuce lokacin da mutane zasu taka doka,saboda jami'an tsaro zasu sanya ido sosai dan ganin anyi abinda ya kamata."

Daga karshe yaja kunnen jami'an tsaron da karsu sake ayi amfani dasu wajen kawo rudu a lokacin gudanar da zaben.

Sannan ya shawarci masu zabe dasu kiyaye karsu haure inda hukumar zabe ta INEC ta kayyade musu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel