EFCC za ta gurfanar da tsohon sakataren gwmnatin tarayya Babachir a ranar Talata

EFCC za ta gurfanar da tsohon sakataren gwmnatin tarayya Babachir a ranar Talata

Wata babbar kotun Abuja da ke Maitama ta sanya ranar 12 ga watan Fabrairu a matsayin ranar gurfanar da tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da wasu biyar.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) za ta gurfanar da Lawal a gaban Justis Jude Okeke kan wasu tuhume-tuhume 10 da suka hada da damfara tare da Hamidu David Lawal, Suleiman Abubakar da wasu kamfanoni biyu, Rholavision Engineering Ltd da Josmon Technologies Ltd.

A tuhume-tuhumen da Offem Uket ya cike a ranar 30 ga watan Janairu, an zargi Lawal da hada kai tare da Hamidu, wani darakta a Rholavision da kuma Abubakar, ma’aikaci a wannan kamfanin, don damfarar wasu kudade don haka sun aikata laifin da ya saba ma sashi 26(1)(c) na aikata rashawa da wasu laifufuka da suka saba ma doka ta 2000 da kuma sashi 12.

EFCC za ta gurfanar da tsohon sakataren gwmnatin tarayya Babachir a ranar Talata

EFCC za ta gurfanar da tsohon sakataren gwmnatin tarayya Babachir a ranar Talata
Source: Depositphotos

Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya zargi Hamidu, Abubakar da Rholavision da karban kwangilar cire ciyawa zuwa kamfanin holavision Engineering Ltd daga ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya ta shirin tallafi na fadar Shugaban kasa a arewa maso gabas wanda ya kai naira miliyan 6.4.

KU KARANTA KUMA: Mahaifiyar Osinbajo ta yi wa ma su sukar Buhari da danta raddi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Oktoba 2017, ya salami Lawal biyo bayan wani rahoto na bincike da kwamiti karkashin jagorancin Yemi Osinbajo suka gabatar akan zargin zambar sa ake yi masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel