Zaben 2019: Gwamnatin tarayya za ta kulle makarantu 109 don gudun ko-ta-kwana

Zaben 2019: Gwamnatin tarayya za ta kulle makarantu 109 don gudun ko-ta-kwana

Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin kulle garkame kwalejojin sakandari mallakin gwamnatin tarayya su dari da tara, domin gudun ko ta kwana sakamakon babban zaben gama gari na 2019 dake karatowa, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta labarto daga ranar Laraba mai zuwa ne za’a kulle makarantu, haka zalika ana bukatar kowane dalibi ya koma gida, har sai bayan zaben, wanda za’a fara daga ranar 16 ga watan Feburairu zuwa ranat 2 ga watan Maris.

KU KARANTA: Kuna kiran masoyanku su sosu don Allah, kuna sonsu don kudi – Naziru ga A Zango

Gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin kare dalibai daga samun kansu cikin runtsin siyasa a daililin rikici ko tashin hankali tsakanin magoya jam’iyyun siyasa mabanbanta da ka iya biyo zaben 2019.

Kaakakin ma’ikatan ilimi, Ben Goong ya tabbatar da rahoton, inda yace nan bada jimawa ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu zai sanar da hutun a hukumance a ranar Juma’a, 8 ga watan Feburairu.

“Na so na sanar da ranar hutun a ranar Alhamis, amma ministan ilimi zai tattauna da manema labaru a ranar Juma’a, kuma zai tabo batun hutun.” Inji Kaakakin ma’ikatan ilimi, Mista Ben Goong.

Bugu wasu majiyoyi sun tabbatar da batun shiga hutun makarantun gwamnatin tarayya, inda ko a yanzu haka wasu manyan makarantu masu zaman kansu dake cikin garin Abuja sun fara rufewa, yayin da wasu manyan makarantun gaba da sakandari a fadin kasar suka sanar da hutun zabe.

Majiyoyi sun tabbatar da cewar idan har aka kulle kwalejojin gwamnatin tarayya kamar yadda ake rayawa, toh tabbas ba za’a budesu ba har sai ranar 4 ga watan Maris, bayan kammala zaben gwamnoni da yan majalisun jihohi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel