Toh fa! Ba zamu dage zaben 2019 ba – Inji hukumar INEC

Toh fa! Ba zamu dage zaben 2019 ba – Inji hukumar INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta tabbatar ma yan Najeriya cewa za ta gudanar da zaben gama gari na 2019 kamar yadda ta shirya, don haka ba za ta dage zaben kamar yadda wasu yan siyasa ke kiraye kiraye ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar zabe a ofishinsa dake babban birnin tarayya Abuja, inda yace duk da shari’un dake gaban kotu akan zaben fidda gwani na jam’iyyu, INEC ba zata dage zabenba.

KU KARANTA: Kuna kiran masoyanku su sosu don Allah, kuna sonsu don kudi – Naziru ga A Zango

Legit.ng ta ruwaito Farfesa Mahmood ya dauki alkawarin ba zai saba ma umarnin kotu ba, kuma ba zai ji shayin sauke nauyin daya rataya a wuyansa ba. “Kararrakin dake gaban kotu wanda suka samo asali dage zaben fidda gwanin jam’iyyun siyasa sun kai guda 640.

“Sau 640 aka shigar da karar INEC, an aiko mana da bukatar samar da sahihan sakamakon zabukan har sai 540, sa’annan an aiko mana da takardun korafe korafen yadda aka gudanar da zabukan shuwagabannin jam’iyyu da na fidda gwani guda 186.

“Yana daga cikin aikin INEC yin biyayya ga umarnin kotu, amma ba zamu dage zaben 2019 saboda wani umarnin kotu ba, sai dai zamu samar da nagartattun matakan da zamu dauka idan har wata kotu ta bada yanke hukunci yayin da ake gab da zabe.” Inji shi.

Haka zalika shugaban ya tabbatar da amfanin na’urar ‘Card reader’ wajen tantance katin zabe, wanda hakan zai tsaftace zaben tare da kara masa sahihanci, sai dai ya yi mamakin yadda wasu jama’a ke korafin rashin samun katukan zabensu.

Ya kara da cewa INEC ta buga katin zabe guda miliyan 14 da dubu dari biyu tun bayan rufe rajistan katin zabe a bara, don haka yace akwai yiwuwar hukumar za ta kara wa’adin kwanakin karbar katin ga jama’a.

Daga karshe yace INEC ta bada fifiko ga tsofaffi da gajiyayyu, mata masu dauke da juna biyu da kuma masu nakasa a wajen kada kuri’u a rumfunan zabe, don haka yace akwai bukatar jama’a su baiwa hukumar goyon baya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel