Wasu miyagun mutane sun kulla shirin halaka El-Zakzaky a hannun jami’an tsaro

Wasu miyagun mutane sun kulla shirin halaka El-Zakzaky a hannun jami’an tsaro

Kungiyar yan shia ta Najeriya, IMN, ta fallasa wata kullalliyar shirin da tace wasu miyagu na kullawa don ganin sun halaka jagoransu, Malam Ibrahim Yakubu El-Zakzaky, a inda yake tsare, tun bayan kamashi da gwamnatin Najeriya ta yi a shekarar 2015.

Sakataren watsa labarum kungiyar, Abdullahi Musa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar yayin ganawarsa da manema labaru a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu, inda yace sun samu wani rahoton sirri dake nuna yunkurin da ake yi na kashe El-Zakzaky.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya kwaci Buba Marwa daga hannun yan jagaliyan da kyar a Adamawa

Musa yace sun samu bayanin wata wasika da wani mutum, Sunusi M Galadima, Daraktan tsaron cikin gida a ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkar tsaro, NSA, ya aika ma babban sufetan Yansanda, game da shirin wasu fursunoni na kai ma Zakzaku hari, tare da kasheshi.

“A ranar 8 ga watan Agustan bara mun samu labarin hukumar DSS ta shirya amfani da wasu fursunoni da zasu kai ma Zakzaky hari tare da matarsa a inda take tsare dasu, sai dai basu samu nasarar aiwatar da shirin nasu ba, sai ga shim un sake samun wani rahoton dake nuna ofishin NSA ta shirya wata sabuwar shirin kashe Zakzaky, sai dai wannan karo zasu daura laifin akan mabiyan Zakzaky ne.” Inji shi.

Da wannan ne Musa yayi kira ga kasashen duniya da su kama shugaban kasa Muhammadu Buhari idan wani mugun abu ya samu Zakzaky, saboda a cewarsu da sa hannun shugaba Buhari ake kokarin kashe malaminsu.

Haka zalika kungiyar ta musanta rahotannin dake dangantasu da wani rahoto dake cewa wai sun yi hasashen shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fadi zabe a yankin Arewacin Najeriya, daga karshe kuma yace zasu cigaba da tawaye har sai an sako Zakzaky da matarsa.

A yanzu haka dai ana cigaba da sharia tsakanin gwamnatin jahar Kaduna a bangare daya, da shugaban kungiyar yan shia Ibrahim Zakzaky da kungiyar a bangare guda, inda gwamnatin jahar ke zarginsa Zakzaky da tayar da hankali a Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel