Saura kwanaki 8 zaben 2019: Muna so INEC ta dage zaben jihar Rivers - APC

Saura kwanaki 8 zaben 2019: Muna so INEC ta dage zaben jihar Rivers - APC

- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta dage zabukan jihar

- INEC ta haramtawa APC gabatar da 'yan takara a zabukan masu zuwa sakamakon rikicin da ya mamaye zabukan fitar da gwani na jam'iyyar da ya gudana

- Jam'iyyar ta ce Nyesom Wike, gwamnan jihar, ya na amfani da rikicin da APC ke yi a jihar domin cimma manufarsa

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta dage zabukan jihar.

Hukumar INEC ta haramtawa APC gabatar da 'yan takara a zabukan masu zuwa sakamakon rikicin da ya mamaye zabukan fitar da gwani na jam'iyyar da ya gudana.

A yanzu dai akwai tsagin jam'iyyar guda biyu. Daya na karkashin Rotimi Amaechi, ministan zirga zirga yayin da Magnus Abe, sanata mai ci a yanzu, ke jagorantar dayan bangaren.

Tonye Princewill, daraktan watsa labarai na yakin zaben Tonye Cole, dan takarar gwamnan jihar a inuwar tsagin jam'iyyar APC karkashin Amaechi, ya ce gudanar da zabe a jihar ba tare da sanya APC ba wani lamari ne da ba zai taba sabuwa ba.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Fayose ya caccaki EFCC kan gaza gurfanar da Babachir Lawal

Saura kwanaki 8 zaben 2019: Muna so INEC ta dage zaben jihar Rivers - APC

Saura kwanaki 8 zaben 2019: Muna so INEC ta dage zaben jihar Rivers - APC
Source: Twitter

Ya ce baiwa 'yan takarar APC karin wa'adi na karkare gudanar da yakin zabensu ya zama wajibi saboda tsaikon da aka samu bisa bin dokoki da wasu tsare tsare na zaben kasar.

"Duk da cewa har yanzu babu sunanmu a cikin jam'iyyu masu gabatar da 'yan takara, muna kan ganin anyi hakan. A yanzu INEC ta karbi umurni na farko kuma nan da kwana daya ko biyu zata samu umurni na biyu," a cewarsa.

Sanarwar ta ce duba da irin abubuwan da suke kan faruwa a jihar, ya kamata a gudanar da zaben jihar ne a ranar 2 ga watan Maris.

Sanarwar ta kara da cewa Nyesom Wike, gwamnan jihar, ya na amfani da rikicin da APC ke yi a jihar domin cimma manufarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel