Fadan manya: Ni ma biloniya ne kafin na zama gwamna - Ortom ya caccaki Akume

Fadan manya: Ni ma biloniya ne kafin na zama gwamna - Ortom ya caccaki Akume

- Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce ya shiga harkar siyasa, kuma har ya zama gwamnan jihar ba wai don ya saci kudin jama'a ya azurta kansa ko iyalansa ba

- Wannan bayanin, ya biyo bayan zargin da Sanata Akume ya yiwa Ortom na yin amfani da ofishinsa na gwamna, wajen sace kudaden jihar domin azurta kansa

- Sai dai Ortom ya bugi kirji da cewa tuni shi biloniya ne ko kafin ya zama gwamnan jihar Benue

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce ya shiga harkar siyasa, kuma har ya zama gwamnan jihar ba wai don ya saci kudin jama'a ya azurta kansa ko iyalansa ba, yana mai cewa tuni shi biloniya ne ko kafin ya zama gwamnan jihar Benue.

Ortom, wanda ya zanta da manema labarai, ya yi wannan jawabin ne a matsayin martani ga Sanata George Akume, wanda ya yi wani zargi da kuma caccakar Ortom a lokacin yakin zaben shugaban kasa Buhari da ya gudana a filin wasanni na Aper Aku da ke Makurdi a ranar Laraba.

Sanata Akume ya zargi Ortom da yin amfani da ofishinsa na gwamna, wajen sace kudaden jihar domin azurta kansa.

Akume ya ce: "A yau, akwai wani gwamna a Arewa ta tsakiya, (wanda ya ke nufin Ortom) wanda ya fi Buhari arziki kuma ya fi Buhari kudi. Kuma kowa ya san yadda ya tara kudinsa, uwa uba, yadda ya gaza samar da ayyukanyi ga al'ummar jihar."

KARANTA WANNAN: Saura kwanaki 8 zaben 2019: Muna so INEC ta dage zaben jihar Rivers - APC

Fadan manya: Ni ma biloniya ne kafin na zama gwamna - Ortom ya caccaki Akume

Fadan manya: Ni ma biloniya ne kafin na zama gwamna - Ortom ya caccaki Akume
Source: Facebook

Sai dai a na shi martanin, Ortom ya caccaki Akume, inda ya bayyana cewa ya kamata ace sanatan na garkame a cikin bursuna yanzu, saboda zargin da ake masa na sace N2bn a lokacin da ya ke cikin gidan gwamnatin jihar a 2007.

Ortom ya ce, "Maganar gaskiya anan ita ce Akume bai isa ya ce nine silar gaza samar da ayyuka a jihar Benue ba; ko kafin na zama gwamna, ni biloniya ne.

"Kafin na zama minista, na ajiye aikina na shugaban kamfanina kuma kamfanin na gudanar sa ayyukansa cikin san barka. Na ciyo bashi daga bankin Nexim, bankin masana'antu da babban bankin Nigeria.

"Amma shi Akume ya yi gwamna na tsawon shekaru 8, bai tsinana komai ba illa sace N2bn kafin ya bar ofis; har zuwa yanzu, yana fuskantar tuhuma a hannun EFCC kafin ya koma APC, babu wani abu da aka yi akai."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel