Babbar magana: Fayose ya caccaki EFCC kan gaza gurfanar da Babachir Lawal

Babbar magana: Fayose ya caccaki EFCC kan gaza gurfanar da Babachir Lawal

- Ayodele Fayose, ya tambayi hukumar EFCC dalilin da ke kawo tsaiko na gurfanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal

- A watan Janairu, EFCC ta shigar da karar tsohon SGF a babbar kotun Abuja kan zarginsa da aikata laifuka 10

- Hukumar EFCC dai ta gurfanar da Mr Oke da matarsa akan bakalar $43,449,947, £27,800 da kuma N23,218,000 da aka alakantasu da sa hannu a ciki

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a ranar Alhamis, ya tambayi hukumar nan da ke yaki da cin hanci da rashawa da kuma barayin kudin gwamnati, (EFCC) kan dalilin da ke kawo tsaiko na gurfanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.

A shafinsa na Twitter, Fayose ya yi mamakin irin yadda za a ce duk da gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na hukunta Lawal, amma hukumar EFCC ta gaza tabuka komai akan zargin da ake yi masa.

Ya tambayi hukumar EFCC ko tana jira ne sai Lawal ya fice daga kasar, kamar yadda tsohon daraktan hukumar tsaro ta kwararru na kasa NIA, Ambasada Ayo Oke da matarsa, Folashade suka yi, inda suma duk da zargin da ake yi masu, suka tsallaka suka bar kasar.

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: Atiku ya lashi takobin kammala ginin tashar samar da lantarki ta Mambilla

Babbar magana: Fayose ya caccaki EFCC kan gaza gurfanar da Babachir Lawal

Babbar magana: Fayose ya caccaki EFCC kan gaza gurfanar da Babachir Lawal
Source: Depositphotos

Ya ce: "Ina da tambayar da na ke so na yiwa hukumar INEC, muna sane da cewa wannan gwamnatin a shirye take ta hukunta tsohon SGF, Babachir Lawal, shin suna jira ne har sai ya fice daga kasar? Idan har sun yi ikirarin cewa tsohon shugaban NIA, Oke da matarsa sun tsere zuwa kasar waje, shin tsohon SGF ya tsere ne a yanzu?"

Hukumar EFCC dai ta gurfanar da Mr Oke da matarsa akan bakalar $43,449,947, £27,800 da kuma N23,218,000 da aka alakantasu da sa hannu a ciki.

A zaman da wata kotu ta yi a ranar Alhamis, wacce ta bayar da izinin cafko ma'auratan, bayan da EFCC ta gaza gabatar da su a gabanta ba sau daya ba sau biyu ba, ya bayyana cewa ma'auratan da ake tuhumar sun tsallake sun bar kasar.

Kudurin gwamnatin tarayya na hukunta Babachir Lawal ya bayyana ne a lokaci daya dana Ayo Oke.

A watan Janairu, EFCC ta shigar da karar tsohon SGF a babbar kotun Abuja kan zarginsa da aikata laifuka 10.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel