A cigaba da zagayen kananan hukumomin jihar Kano 44 da ya ke yi domin kaddamar yakin neman sake zaben sa a karo na biyu, gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci kananan Dala, Gwale, da Municipal a yau, Alhamis.
Dubban jama'a ne su ka fito domin tarbar gwamnan da kuma halartar wurin taron yakin neman zaben sa a kananan hukumomin da su ka ziyar ta.
Yayin taron kamfen din, an ji wasu matasa na yiwa gwamna Ganduje kirari "uban Abba", a wani salo na nuna cewar gwamnan gaba ya ke da babban abokin hamayyar sa, Abba Kabir Yusif, dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Kamfen din Ganduje a cikin birnin Kano
Source: Twitter

Kamfen din Ganduje a cikin birnin Kano
Source: Twitter

Kamfen din Ganduje a cikin birnin Kano
Source: Twitter

Kamfen din Ganduje a cikin birnin Kano
Source: Twitter
A yayin da ya rage saura 'yan kwanaki kadan a fara gudanar da zabukan shekarar nan da mu ke ciki, 'yan siyasa, musamman 'yan takara, na cigaba da yaki neman zabe.
DUBA WANNAN: INEC ta fara raba muhimman kayan aikin zabe
Ana ganin takarar zaben gwamna a jihar Kano zai fi zafe ne tsakanin 'yan takara 3; Gwamna Ganduje a jam'iyyar APC, Abba Kabir Yusif a jam'iyyar PDP, da kuma Malam Salihu Sagir Takai a jam'iyyar PRP.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng