Mahaifiyar Osinbajo ta yi wa ma su sukar Buhari da danta raddi

Mahaifiyar Osinbajo ta yi wa ma su sukar Buhari da danta raddi

- Mahaifiyar mataimakin sugaban kasa Yemi Osinbajo, Olubisi Osinbajo, tace gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci tazarce

- Olubisi tace duk wanda yace basu yi aiki ba toh ba a duniyar nan yake ba

- Ta kuma yi godiya ga Allah da ya kare mata danta bayan hatsarin jirgin sama da suka yi a ranar Asabar

Mahaifiyar mataimakin sugaban kasa Yemi Osinbajo, Olubisi Osinbajo, tace gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cancanci tazarce.

Ta bayyana hakan ne a ranar Alamis, 7 ga watan Fabrairu lokacin dad anta ya ziyarceta a yayin kamfen dinsa na gida-gida a yankin Somolu da ke jihar Lagas.

Mahaifiyar Osinbajo ta yi wa ma su sukar Buhari da danta raddi

Mahaifiyar Osinbajo ta yi wa ma su sukar Buhari da danta raddi
Source: Depositphotos

Matar mai shekaru 85 a duniya tace nasarorin sa gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu yai wanda gwamnatocin baya suka samu a shekaru 16.

Ta kuma yi godiya ga Alla da ya bar danta da rai bayan hatsarin jirgin sama da yayi a jihar Kogi a ranar Asabar da ya gabata.

“Sun yi kokari. Duk wanda yace basu yi komai, to lallai wannan mutumin ba a duniyar nan yake ba, sai dai idan a wata duniyar yake saboda sunyi kokari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Za a rufe hanyoyi 18 a Lagas saboda Buhari

“Abunda Buhari da Osinbajo suka yi a shekaru uku shine wanda wasu suka gaza yi a shekaru 16. Mun godiya ga Alla kuma za mu ci gaba da gode ma Allah bayan zabe” inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel