Walter Onnoghen: Mun gano $30,000 da wani lauya ya turawa tsohon babban Alkalin - EFCC

Walter Onnoghen: Mun gano $30,000 da wani lauya ya turawa tsohon babban Alkalin - EFCC

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gano kudi $30,000 da wani babban lauya Joe Agi ya tura asusun bankin Jastis Walter Onnoghen, shugaban alkalan Najeriya da Buhari ya sallama.

Ya kara bayyana cewa Onnoghen bai bayyana wata asusun banki da ya mallaka a Heritage Bank ba, wani karin sabawa dokar Najeriya.

Joe Agi na daya daga cikin lauyoyin da ke tsayawa Walter Onnoghen a gaban kotun CCT.

Wannan sabon bincike na cikin wasikar da hukumar EFCC ta aikawa majalisar shari'an Najeriya domin laddabtar da Onnoghen, kari akan zargin da ake tuhumarsa da shi.

Majiya a NJC ya bayyanawa jaridar Cable cewa an turawa Onnoghen kudi $30,000 ne a shekarar 2009 bayan an gano wasu makudan kudi da aka tura tsakanin shekarar 2011 da 2013 lokacin zabe.

KU KARANTA: Yadda mutan jihar Taraba da Adamawa suka tarbi shugaba Buhari

Mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen kuma ya nada Ibrahi Tanko Muhammad a matsayin mukaddashi.

Za ku tuna cewa gwamnatin shugaba Buhari tana tuhumtar Jastis Onnoghen da laifin rashin bayyana wasu kudade a asusun banki shida duk da kasancewarsa ma'aikacin gwamnati.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci hukumar leken asirin kudaden sata wato Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) da ta daskarar da asusun bankin shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, guda biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel