Kamfe: Tururuwar al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Katsina

Kamfe: Tururuwar al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Katsina

A yau Alhamis 7 ga watan Fabrairu, 2019, mun kawo muku rahoton yadda dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Daura; Dakta Umar Faruk.

Tururuwar al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Katsina

Tururuwar al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Katsina
Source: Twitter

Jihar Katsina cikin cikar ta batsewa yayin yakin zaben Atiku

Jihar Katsina cikin cikar ta batsewa yayin yakin zaben Atiku
Source: Twitter

Atiku akan mimbarin girgiza magoya baya

Atiku akan mimbarin girgiza magoya baya
Source: Twitter

Atiku tare da shugaban PDP akan mimbarin girgiza magoya baya cikin birnin Katsinan Dikko

Atiku tare da shugaban PDP akan mimbarin girgiza magoya baya cikin birnin Katsinan Dikko
Source: Twitter

Dandazon al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Katsina

Dandazon al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Katsina
Source: Twitter

Yayin isowar tawagar Atiku domin yakin zabe a jihar Katsina

Yayin isowar tawagar Atiku domin yakin zabe a jihar Katsina
Source: Twitter

Kamar yadda ajiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Atiku bayan ziyarar sa ta ban girma ya kuma fatsama cikin birnin Katsinan Dikko inda ya gudanar da taron sa na yakin neman zaben a filin wasanni na Karkanda.

Taron neman magoya baya da tsohon mataimakin shugaban kasar ya gudanar ya yi armashi yayin da tawagar sa ta hadar da tsohon gwamnan jihar, Barrista Ibrahim Shehu Shema da kuma shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Osinbajo ya ziyarci iyalan marigayi Manjo Solomon Kabiru Umaru

Kazalika jagoran kungiyar yakin neman zaben Atiku kuma shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, ya halarci babban taron domin girgiza magoya baya yayin da babban zaben kasa ya karato.

A yayin da Atiku ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe cikin jihar Katsina, kazalika shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya gudanar da na sa taron a birnin Yola na jihar Adamawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel