Zabe: Ba mu da dan takara a Najeriya – Gwamnatin Amurka

Zabe: Ba mu da dan takara a Najeriya – Gwamnatin Amurka

Babban jakadan kasar Amurka a Najeriya, Ambasada John Bay, ya ce damuwar gwamnatin kasar Amurka shine ganin an yi sahihin zabe mai tsafta a Najeria, ba batun goyon bayan wani dan takara ba.

Ambasada Bay ya ce Amurka ba ta goyon wani dan takarar shugaban kasa a Najeriya a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Fabarairu.

Fidelis Soriwei, mai taimakawa gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dikson, a bangaren yada labarai da hulda da jama’a, ne ya rawaito cewar Amabasada Bay ya fadi hakan ne yayin wata ziyara da ya fadar gwamnatin jihar Bayelsa da ke Yenagowa a jiya, Laraba.

Zabe: Ba mu da dan takara a Najeriya – Gwamnatin Amurka

Manyan 'yan takara a Najeriya – Atiku da Buhari
Source: Twitter

Soriwei ya kara da cewa Ambasada Bay ya ziyarci jihar ta Bayelsa ne a rangadin da yak e a jihohin kudancin Najeriya domin gana wa da sarakunan gargajiya da ma su ruwa da tsaki a siyasa a kan muhimmancin gudanar da zabe cikin lafiya da lumana.

DUBA WANNAN: Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters

Amurka ba ta da wani dan takara a zaben Najeriya. Damuwar mu ita ce a yi zabe sahihi mai tsafta da zai kasance shine zabin ‘yan Najeriya.

“Na ziyarci jihar Bayelsa ne domin tattauna wa da gwamna a kan muhimman batutuwa daban-daban kafin na wuce zuwa zuwa Fatakwal gobe,” a kalaman Ambasada Bay.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel