Sayar da katin zabe: Jami’an DSS sun kama ma’aikatan INEC 2

Sayar da katin zabe: Jami’an DSS sun kama ma’aikatan INEC 2

Hukumar tsaro ta farin kaya a jihar Ribas ta gurfaar da wasu ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) a gaban wata kotun majistare da ke Fatakwal bias zargin su da laifin sata tare da sayar da katin zabe (PVC) 3,097 da ke ofishin INEC.

An gurfanar da ma’aikatan na INEC da ke aiki a karamar hukumar Opobo Nkoro tare da wani dan siyasa a yau, Alhamis.

Kazalika, an gurfanar da wani matashi mai shekaru 25 bayan samun sa da laifin yin sojan gona a matsayin ma’aikacin INEC tare da damfarar jama’a N3,800 bisa yaudarar su da cewar zai samar ma su aiki.

A yau ne Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa (INEC) ta fara rabon gamagari da muhimman kayan aikin zabe ga jihohi.

Sayar da katin zabe: Jami’an DSS sun kama ma’aikatan INEC 2

katin zabe
Source: UGC

Kwamishina hukumar sannan shugaban kwamitin wayar da kan ma su zabe, Festus Okoye, ne ya sanar da a jiya, Laraba, yayin wata tattauna wa da manema labarai a hedikwatar INEC ta kasa da ke Abuja.

A cewar sa, hakan ya nuna cewar hukumar INEC ta shirya tunkarar zabukan da za a fara cikin watannan.

DUBA WANNAN: Kamfen din Buhari: An kasha mutane 5, an kai wa tawagar gwamna hari

"A yau, Laraba, da nake magana da ku a yanzu haka, an kai kayayyakin aikin zabe zuwa dakunan adana kaya manyan yankunan kasar nan. Wasu kayan tuni an mika su ga jihohi da ofisoshin kananan hukumomi," a cewar Okoye.

Wasu daga cikin gama garin kayan aikin zabe sun hada da akwatin kuri'u, kayan rubutu, kayan ma'aikatan wucin gadi da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel