Yanzu-yanzu: ASUU ta dakatad da yajin aiki, dalibai su koma makaranta

Yanzu-yanzu: ASUU ta dakatad da yajin aiki, dalibai su koma makaranta

Kungiyar malaman jami'o'in gwamnati ASUU ta dakatad da yajin aiki da aka kwashe watanni uku anayi yanzu bayan sulhu da gwamnatin tarayya.

Mun kawo muku cewa kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya sun cimma matsaya domin kawo karshen yajin aikin da ya hana daliban jami'a samun karatu a fadin tarayya.

Legit Hausa ta samu wannan labari da yammacin Alhamis, 7 ga watan Febrairu, 2019 bayan ganawar wakilan kungiyar ASUU da na gwamnatin tarayya karkahin jagorancin ministan kwadago, Chris Ngige.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ne ya sanar da janye yajin aikin yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja, birnin tarayya.

KU KARANTA: Yayinda Atiku ya tafi Daura yau, Buhari ya dira jihar Adamawa

ASUU ta ce ta janye yajin aikin ne bayan kamala tuntuba da tattauna wa a kan tayin da gwamnatin ta yi a kan bukatun da kungiyar ta bukaci a cika ma ta kafin ta koma bakin aiki.

A sanarwar da ta fitar, ASUU ta ce bayan amince wa da gwmnatin tarayya ta yi na sakin biliyan N20 domin biyan malaman jami’o’I bashin alawus da su ke bi a shekarar 2018, gwamnatin ta yi alkawarin sake fitar da wata biliyan N25bn a watan Afrilu zuwa Mayu na shekarar nan, bayan haka kuma gwamnatin za ta cigaba da zartar da yarjejeniyar da su ka kulla da ASUU tun shekarar 2013.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel