Malaman addini sun bukaci yan Najeriya da su zabi Buhari

Malaman addini sun bukaci yan Najeriya da su zabi Buhari

- Wasu malaman addini a fadin manyan addinan kasar sun bayyana cewa Allah ne ya zabi Buhari domin yayi mulki tsawon shekaru takwas

- Shugaban kungiyar yayi kira ga yan Najeriya da su ida nufin Ubangiji ta hanyar marawa Buhari baya a karo na biyu

- Bishop Garuba yaceBuhari ya nuna kulawa ga yan Najeriya mabukata ta hanyar da samar da tsaro da kuma shirin tallafawa jama'a

Kimanin malaman addini 1000 a fadin manyan addinn Najeriya ne suka halarci wani gangami a Abuja domin nuna goyon baya ga kudirin tazarcen dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wato Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugabannin addinin a karkashin kungiyar National Inter-Faith and Religious Organizations for Peace (NIFROP), sunce Allah ne ya zabi Buhari domin ya mulki Najeriya na tsawon shekaru takwas sannan ya kamata a bari ya cika wannan umurni na Ubangiji, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Malaman addini sun bukaci yan Najeriya da su zabi Buhari

Malaman addini sun bukaci yan Najeriya da su zabi Buhari
Source: UGC

Shugaban NIFROP yace Buhari ya nuna kulawa ga yan Najeriya mabukata ta hanyar da samar da tsaro da kuma shirin tallafawa matasa na N-Power, ciyar da dalibai yan makaranta, bayar da tallafi ga masu kananan sana’o’i, da dai sauran shirye-shirye da talakawa suka amfana.

KU KARANTA KUMA: Atiku: Lamidon Adamawa ya goyi bayan Buhari

A halin da ake ciki, mun ji cewa Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta zabi Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasa da za ta marawa baya a babban zaben 2019.

An cimma wannan yarjejeniyar ne tsakanin jam'iyyar SDP a wurin taron majalisar zartarwa na jam'iyyar. A halin yanzu ana cigaba da taron a babban birnin tarayya Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel