Kamfen din Buhari: An kasha mutane 5, an kai wa tawagar gwamna hari

Kamfen din Buhari: An kasha mutane 5, an kai wa tawagar gwamna hari

A kalla mutane 5 ne rahotanni su ka bayyana cewar sun rasa ran su a yau, Alhamis, yayin kaddamar da yakin neman zaben da shugaba Buhari ya yi a jihar Taraba. Wasu mutane biyu na cikin mawuyacin hali.

Kazalika an kai wa tawagar gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, farmaki yayin da tawagar gwamnan da ta mataimakin sa da hadimansu su ka raka shugaba Buhari filin jirgi na Danbaba Sunati bayan ya kamala kamfen.

An lalata kusan dukkan fastocin gwamnan da na Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, da ke garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, Bala Dan Abu, mai taimakawa gwamna Ishaku a bangaren watsa labarai, ya yi Alla-wadai da abinda ya faru tare da dora laifin a kan jami’an tsaro.

Kamfen din Buhari: An kasha mutane 5, an kai wa tawagar gwamna hari

Kamfen din Buhari
Source: UGC

Sun lalata motar da mataimakin gwamna ke ciki da ma wasu da dama da ke ayarin mataimakin gwamnan, har da motar kwamishinan ‘yan sanda da ta mai bawa gwamna shawara ba su kyale ba.

“Sun debo hayar ‘yan daba da muggan makamai daga jihohi daban-daban domin su nuna cewar jam’iyyar APC na da dumbin magoya baya a jihar Taraba.

DUBA WANNAN: INEC ta fara raba muhimman kayan aikin zabe

“Sun zo dauke da bindigu, adda, da itatuwa, su na wasa da su a gaban jami’an tsaro ba tare da shayi ko shakkar komai ba,” a cewar Abu.

Kazalika ya zargi jami’an tsaro da bawa ‘yan dabar kariya yayin da su ka shiga gari domin kawai su lalata fastocin gwamna Ishaku da na Atiku a duk in da su ka gan su.

Abu ya kara da cewa gwamnatin jihar Taraba ba zata cigaba da nade hannu tana kallo ana cin zarafin ta da mutanen ta ba don kawai ba jam’iyyar su daya da shugaban kasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel