Atiku: Lamidon Adamawa ya goyi bayan Buhari

Atiku: Lamidon Adamawa ya goyi bayan Buhari

- Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa ya nuna goyon baya ga tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Sarkin ya bukaci jama'a su kada kuri'un su ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC

- Ya yaba da nasarorin da gwamnati mai mulki ta samu cewa ta cancanci a bata damar kammala ayyukan ci gaba da ta dauko yi

Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, Lamidon Adamawa, a ranar Alhamis 7 ga watan Fabrairu ya yi kira ga yan Najeriya da su yiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kamfen domin tabbatar da ganin dan takarar Shugaban kasa na All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

Atiku: Lamidon Adamawa ya goyi bayan Buhari

Atiku: Lamidon Adamawa ya goyi bayan Buhari
Source: UGC

A wani jaawabi daga kakakin Shugaban asa, Femi Adesina, ya bayyana cewa Lamido wanda ya kasance sarkin dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yace “Ya Shugaban kasa, babu makawa an samu ci gaba sosai a gwmnatin nan amma tabbass kana bukatar Karin lokaci domin cimma manufarka na Najeriya mai inganci. Don haka, akwai bukatar a mara maka baya domin kaiwa mataki na gaba domin ka samu damar aiwatar da shirye-shiryen jam’iyyarka.”

Shugaban kasar dai ya isa mahaifyar babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar adawa ta PDP, a ranan Alhamis, 7 ga watan Febrairu, 2018. A dai-dai wannan lokaci kuma kwamitin kamfen jam'iyyar PDP ta isa garin Daura, mahaifar Buhari.

KU KARANTA KUMA: PDP, CUPP sun fallasa makircin da ake shirin kullawa Atiku da Saraki

A baya mun ji cewa Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta zabi Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasa da za ta marawa baya a babban zaben 2019.

An cimma wannan yarjejeniyar ne tsakanin jam'iyyar SDP a wurin taron majalisar zartarwa na jam'iyyar. A halin yanzu ana cigaba da taron a babban birnin tarayya Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel