Kanawa sun shirya tsaf domin tarbar Atiku - Shugaban PDP

Kanawa sun shirya tsaf domin tarbar Atiku - Shugaban PDP

Shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na jihar Kano, Sanata Masa’ud El-Jubril Doguwa ya ce jam'iyyar ta gama shirye-shiryen tarbar dan takarar shugabancin kasar ta Atiku Abubakar domin kadamar da yakin neman zabensa a jihar.

Ya bayar da tabbacin cewa za a yiwa Atiku irin tarbar da ba a taba yi masa ba a dukkan jihohin da ya ziyarta.

A hirar da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis a Kano, ya ce Atiku zai iso birnin Kano ya tarar da dandazon magoya irin wadda bai taba gani ba a sauran jihohi.

Kanawa sun shirya tsaf domin tarbar Atiku, inji Shugaban PDP na Kano

Kanawa sun shirya tsaf domin tarbar Atiku, inji Shugaban PDP na Kano
Source: UGC

DUBA WANNAN: Abinda na fadawa sarakunan Nasarawa yayin ganawar sirri da mu kayi - Buhari

Mun kammala dukkan shirye-shirye domin tarbarsa da kuma tabbatar da cewa anyi kamfen din an tashi lafiya.

A cewarsa, "Muna son mu tabbatar cewa wannan itace uwa ga dukkan sauran tarukkan da akayi a baya saboda Kano daban ta ke.

"Ina tsamanin wannan taron zai fita daban da sauran domin Kano daban da ke da sauran jihohin Najeriya. Babu wata jiha da za ta iya kamanta kanta da irin taron da za ayi a Kano a ranar Lahadi."

Ya cigaba da cewa: "Ana samun irin wannan a kowace jam'iyyar siyasa. Kano itace cibiyar siyasar Najeriya. Dole mu hada kan mu wuri guda.

"Ana samun banbancin akidu da halaye amma idan ka duba wanda zai zo Kano namu ne, Atiku na Kwankwaso ne saboda haka muna maraba da Atiku.

"Dukkan mu muna goyon bayan Atiku har cikin zuciyarmu domin shi bakon mu ne.

"Zamu tabbatar mun masa tarba irin ta girma da ya dace da shi a matsayinsa na jigo a siyasar Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel