PDP, CUPP sun fallasa makircin da ake shirin kullawa Atiku da Saraki

PDP, CUPP sun fallasa makircin da ake shirin kullawa Atiku da Saraki

- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi zargin cewa ana kulla wani makirci ga dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyarta, Atiku Abubakar inda za a tuhume su da mallakar bindigogi da kuma kisan kai

- Jam’iyyar hadin gwiwa ma ta Coalition of United Political Parties (CUPP) ta koka kan haka a wani jawabinta

- Kakakin PDP yayi Allah wadai da hakan inda ya danganta hakan da tsananin son mulkin yan adawa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta koka kan wani makirci da ake kullawa domin shafawa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyarta, Atiku Abubakar da Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki bakin fenti, inda za a tuhume su da mallakar bindigogi da kuma kisan kai.

Jam’iyyar hadin gwiwa ma ta Coalition of United Political Parties (CUPP) ta koka kan haka a wani jawabi daga kakakinta, Ikenga Ugochinyere, jaridar The Guardian ta ruwaito.

PDP, CUPP sun fallasa makircin da ake shirin kullawa Atiku da Saraki

PDP, CUPP sun fallasa makircin da ake shirin kullawa Atiku da Saraki
Source: Twitter

Legit.ng ta ruwaito cewa kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, yayi zargin cewa an tanadi wasu miyagun mutane da suyi amfani da motocin Atiku da Saraki don haifar da rikici ta hanyar harbin taron jama’a a yankuna daban-daban na kasar.

Jawabin CUPP yayi zargin cewa “wasu yan jam’iyya mai mulki sun fara yiwa wasu motoci fentin jamiyyar adawa dauke da hotunan shugabannin jam’iyyar sannan sun tanadi bindigogi da za a boye a motocin sannan su bi ayari kamfen din jam’iyyar a Kwara, Kogi da adamawa da sauran yankunan kasar da suka zaba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rikicin zabe ba sabon abu bane a Najeriya – Janar Abdulsalami

“Sai yan sanda su binciki motocin sannan su gano makamai. Makircinsu ya hada da diban yan iska domin su tayar da rikici a wannan rana domin a nada wa jam’iyyar adawa suna mai haddasa usuma."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel