Kakakin rundunar soji, Sani Kukasheka, ya ajiye aiki

Kakakin rundunar soji, Sani Kukasheka, ya ajiye aiki

A yau, Alhamis, ne kakakin rundunar sojin Najeriya, Sani Usman Kukasheka, ya bayyana cewar ya yi murabus daga aikin soja biyo bayan karatowar lokacin sa na yin ritaya daga aiki.

A sakon da ya fitar na bankwana, Kukasheka, ya ce; “bayan godiya ga ubangiji, ina mai sanar da rundunar soji da dukkan ma’aikatan ta, musamman na sashen hulda da jama’a, cewar na yanke shawarar ajiye aikin soja daga ranar Juma’a, 8 ga watan Fabrairu, 2019, biyo bayan karatowar lokacina na yin ritaya daga aiki. Ina yi ma ku bankwana.

“Ina son na yi amfani da wannan dama wajen mika godiya ta musamman ga rundunar soji da abokan aiki na bisa soyayya, kauna, da goyon bayan da su ka nuna min a tsawon shekarun fiye da 30 da na yi ina aiki a sashen hulda da jama’a.

Kakakin rundunar soji, Sani Kukasheka, ya ajiye aiki

Sani Kukasheka
Source: Facebook

“Na bayar da gudunmawa ta ga aikin soji, sannan na samu karuwar ilimi, goge wa da sabo da abokai. Ina mai alfahari da cewar na bar aiki cikin mutunci da lumana.”

DUBA WANNAN: Rigimar duniya: Matashi ya kai karar iyayensa saboda sun haife shi babu izinin sa

Kukasheka ya kara da cewa, “duk da rundunar soji ba ta nada sabon darektan da zai jagorancin sashen hulda da jama’a ba, zan mika aiki ga kanal AA Yusuf, shugaban ma’aikatan sashen hulda da jama’a na rundunar soji. Duk da na bar aikin soja bias radin kai na, ina mai fatan alheri da kariyar ubangiji ga rundunar soji. Ina godiya gare ku abokaina, tabbas zan yi kewar ku.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel