Yanzu Yanzu: Rikicin zabe ba sabon abu bane a Najeriya – Janar Abdulsalami

Yanzu Yanzu: Rikicin zabe ba sabon abu bane a Najeriya – Janar Abdulsalami

- Tsohon Shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakaryace koda dai rikicin zabe ba sabon abu bane a Najeriya, yana gargadin yan siyasa da su guje ma tayar da rikici a lokacin zabe

- Abdulsalami ya bukaci dukkanin yan siyasar kasar da su tabbatar da cewa zaman lafiya ya warzu a kasar sannan cewa su yi aiki don tabbatar da zabe na gaskiya da amana

- Yace idan babu zaman lafiya, babu kasa, sannan idan babu kasa, babu zabe

Tsohon Shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), a ranar Alhamis, 7 ga watan Fabrairu yace koda dai rikicin zabe ba sabon abu bane a Najeriya, yana gargadin yan siyasa da su guje ma tayar da rikici a lokacin zabe.

Ya bukaci dukkanin yan siyasar kasar da su tabbatar da cewa zaman lafiya ya warzu a kasar sannan cewa su yi aiki don tabbatar da zabe na gaskiya da amana.

Yanzu Yanzu: Rikicin zabe ba sabon abu bane a Najeriya – Janar Abdulsalami

Yanzu Yanzu: Rikicin zabe ba sabon abu bane a Najeriya – Janar Abdulsalami
Source: Depositphotos

Janar Abdulsalami ya bayar da wannan jawabin nee a wani taron zaman lafiya da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a Abuja mai taken “Peaceful elections and national development” wato “zaben lumana da ci gaban kasa.”

A cewarsa, tsohon Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya tsaya akan zancensa lokacin da ya bayyana cewa shugabanci bai kai darajar jinin kowani dan Najeriya ba.

KU KARANTA KUMA: Mutane 2 sun mutu a wajen gangamin kamfen din Buhari a Jalingo

Janar Abdulsalami ya kuma bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki da su tabbatar da zaman lafiyar kasar, a cewarsa “idan babu zaman lafiya, babu kasa, sannan idan babu kasa, babu zabe.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel