Shari’ar Fayose: An kwantar da shaidan EFCC, tsohon minista a Asibiti

Shari’ar Fayose: An kwantar da shaidan EFCC, tsohon minista a Asibiti

Shari’ar da wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja, take saurara tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose, ta fuskanci cikas a yau Alhamis, 7 ga watan Feburairu.

Wannan shari’a ta gamu da tasgaro ne a yau sakamakon babban shaidan hukumar EFCC, tsohon ministan tsaro a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Musliu Obanikoro yayi nukusanin zuwa kotu sakamakon kwantar da shi da aka yi a asibiti saboda rashin lafiya.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Kotu ta tsige wani Sanatan APC daga kujerarsa, ta bayyana halastaccen dan takara

Shari’ar Fayose: An kwantar da shaidan EFCC, tsohon minista a Asibiti

Obanikoro da Fayose
Source: UGC

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne Musliu Obanikoro ya bayyana gaban kotun, inda ya shaida mata cewa shi da kansa ya kai ma Ayodele Fayose makudaden biliyoyin kudi (N2,200,000,000) da tsohon mashawarcin Jonathan akan harkar tsaro, Sambo Dasuki ya bashi.

Ko a ranar Talatar data gabata ma sai da Obanikoro ya bayyana gaban kotun, inda ya kara tsatstsage mata bayanai game da badakalar da EFCC ke tuhumar Fayose da ita na cin wani kaso daga kudin makamai.

A zaman na yau ne lauyan EFCC, Rotimi Jacobs ya mika ma kotun takardar shaida dake tabbatar da rashin lafiyan Obanikoro tare da tabbacin an kwantar da shi a wani Asibiti dake Ikoyi ta jahar Legas.

Sai dai Alkalin kotun, Mai sharia Mojisola Olatoregun ta gargadi lauyan EFCC daya tabbata gaskiya yake fada mata, kuma ya sani idan karyane, zata sa kwace lasisisn aikin likitan daya rubuta rahoton tare da kulle asibitin kanta.

Haka zalika Alkalin ta yi nemi da cewa lallai sai Obanikoro ya bayyana a gabanta a zama na gaba, idan kuma ba haka ba za ta daureshi tsawon watanni uku a gidan yari. “Kaga daga nan sai a fara kawoshi Asbiti a motar Fursononi” Inji ta.

Bayan nan Alkali Olataregun ta dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Maris, ta kara da cewa “Ya zama dole ya gurfana a gaban kotu a wannan rana, ko kuma na sa a tilasta masa zuwa.”

Wannan kamiyamiya da ake zargin Fayose da ita ya faru ne a shekarar 2014 yayin da ake shirye shiryen gudanar da zaben gwamnan jahar Ekiti, inda ya tsaya takara a jam’iyyar PDP, sai dai a yanzu Obanikoro ya fice daga PDP ya koma APC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel