2019: Ya kamata yankin Arewa maso Gabas ya samar da shugaban kasa - Dogara

2019: Ya kamata yankin Arewa maso Gabas ya samar da shugaban kasa - Dogara

Mun samu cewa Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya, Honarabul Yakubu Dogara, ya yi karin haske dangane da dalilai da suka sanya ya tsananta goyon baya ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Da ya ke zayyana dalilan sa, Dogara ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa shine mafificin zabi da ya cancanci jagorancin kasar a yayin babban zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar da mu ke ciki.

Atiku da Dogara yayin taron yakin neman zabe na jam'iyyar PDP a jihar Bauchi

Atiku da Dogara yayin taron yakin neman zabe na jam'iyyar PDP a jihar Bauchi
Source: Twitter

Dogara yayin kira ga al'umma da su fito kwansu da kwarkwata wajen zaben Atiku, ya ce babban zaben kujerar shugaban kasa wata muhimmiyar dama ta samar da shugaban kasa da ya fiti daga yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Dogara ya yi wannan kira ne yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar cikin garin Bauchin Yakubu a ranar Talatar da ta gabata.

Babban jigon na kasa ya yi kira ga daukacin al'ummar jihar Bauchi akan kada su kuskura wannan babbar dama ta samar da shugaban kasa daga yankin Arewa maso Gabas ta kubce yayin da suke hangen ta ruwa-ruwa.

KARANTA KUMA: Kamfe: Atiku da tawagar sa sun garzaya jihar Kastina

Yayin jaddada yakinin sa da kuma aminci, kakakin majalisar ya ce yana da tabbacin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP zai dawowa da Najeriya dukkanin martabar ta tare da sanya ta bisa turba da tafarki mai tasiri zuwa ga tudun tsira.

Cikin na sa jawaban, Wazirin Adamawa ya sha alwashin inganta tsaro a yankunan Arewa maso Gabashin kasar nan da ke ci gaba da fuskantar barazana ta ta'addanci. Ya kuma tunatar da al'ummar jihar dangane da yadda gwamnatin jam'iyyar APC ta gaza ta fuskar cika dukkanin alkawurranta da ta dauka yayin yakin zabe a shekarar 2015.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel