INEC ta tabbatar cewa Jam’iyyar APC ba ta ‘Dan takara a Jihar Ribas

INEC ta tabbatar cewa Jam’iyyar APC ba ta ‘Dan takara a Jihar Ribas

Mun samu labari cewa hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC ta bayyana cewa har yanzu ta na nan a kan matsayar ta na cewa jam’iyyar APC mai mulki ba ta da ‘dan takara a Ribas a zaben bana.

INEC ta tabbatar cewa Jam’iyyar APC ba ta ‘Dan takara a Jihar Ribas

Hukumar zabe za ta hana APC shiga takara a Jihar Ribas
Source: Depositphotos

Kwanaki kadan bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta bada, hukumar zabe na Najeriya tace jam’iyyar APC ba ta cikin wadanda za su shiga zaben gwamna da ‘yan majalisu a jihar Ribas a zaben da za ayi a kwanan nan.

Hukumar INEC ta kasa ta bayyana wannan ne a lokacin da ta sanar da cewa an fara raba kayan da za ayi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa da za ayi a watan nan da kuma zaben gwamnoni da zai biyo baya.

Alkali mai shari’a Ali Gumel na kotun daukaka kara ya bada hukuncin da ke nuna cewa za a maida sunan ‘yan takarar jam’iyyar APC cikin wadanda za su nemi kujerar gwamna da ‘yan majalisar tarayya da dokoki a jihar Ribas.

KU KARANTA: Masoyan Shugaba Buhari za su takawa Atiku burki a Kudancin Najeriya

Sai dai duk da wannan hukunci, INEC ta bayyana cewa har yanzu matakin da ta dauka na hana APC shiga cikin zaben na 2019 yana nan. Kwamishinan INEC da ke wayar da kan jama’a game da harkar zabe ya bayyana haka a jiya.

Jami’in da ke da alhakin yada labarai a hukumar zaben kasar, Barista Festus Okoye, yace har yanzu ra’ayin INEC bai canza ba game da batun zaben jihar Ribas. Okoye ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da ‘yan jarida a Abuja.

Har kawo jiya dai, INEC tace abin da ta sani shi ne babu wani ‘dan takaran APC da zai shiga zabe a jihar Ribas. Hukumar tace idan har za ta dauki wani mataki, za ta sake zama domin duba lamarin kafin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel