Da dumi dumi: Kotu ta tsige wani Sanatan APC daga kujerarsa, ta bayyana halastaccen dan takara

Da dumi dumi: Kotu ta tsige wani Sanatan APC daga kujerarsa, ta bayyana halastaccen dan takara

Wani Sanatan jam’iyyar APC, David Umoru daga jahar Neja, ya taba kasa tun kafin zaben, yayin da wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta saukeshi daga kan kujerar takara, inda ta bayyana Mohammed Musa 313 a matsayin halastaccen dan takarar Sanatan mazaban Neja ta gabas.

Da wannan hukuncin, kotun ta haramta ma Sanata David Umoru sake tsayawa takarar Sanata a karo na biyu kenan, bayan ta tabbatar da Mohammed 313 a matsayin halastaccen dan takarar daya lashe zaben fidda gwanin APC na takarar Sanata.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya baiwa jahar Zamfara N60,000,000,000 a matsayin biyan bashi

Da dumi dumi: Kotu ta tsige wani Sanatan APC daga kujerarsa, ta bayyana halastaccen dan takara

Sanata David
Source: Depositphotos

Kotun ta bayyana gamsuwarta da cewa a zaben fidda gwanin yan takarar Sanata da APC ta shirya a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2018, Mohammed 313 ne ya samu kuri’u dubu talatin da tara da dari da casa’in da biyu, 39,192, yayinda David Umoru ya samu kuri’u dubu biyar da dari takwas da saba’in, 5,870.

Da wannna ne kotun ta tabbatar da nasarar Mohammed, amma fa bayan ta caccaki jam’iyyar APC, inda ta bayyana rashin jin dadinta da yadda APC ta yi ma kundin tsarin mulkin Najeriya kaca kaca tare da raina hankulan jama’a ta hanyar sanar da David a matsayin wanda ya samu nasara bayan ga kuri’un Mohammed.

“Shuwagabannin APC sun nuna rashin gaskiya, tare da yi ma dokokin zabe karan tsaye, da kuma dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya gaba daya, don haka duk wani mataki daya saba ma kundin dokokin zabe ko kundin tsarin mulkin mulkin Najeriya ba zai samu gindin zama ba, ba zamu kyaleshi ba.” Inji Alkalin.

Wannan hukuncin kotu ya zo ne a daidai lokacin da Sanata David Umoru ke shirye shiryen sake cin zabe a zaben Sanatoci da zai gudana a rana daya na zaben shugaban kasa, ranar 16 ga watan Feburairu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel