Mutane 2 sun mutu a wajen gangamin kamfen din Buhari a Jalingo

Mutane 2 sun mutu a wajen gangamin kamfen din Buhari a Jalingo

Rahotanni sun kawo cewa mutane biyu sun rasa ransu a ranar Alhamis, 7 ga watan Fabrairu lokacin gangamin kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Jalingo, babbar birnin jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne sanadiyar yawan mutanen da suka halarci wajen taron na Jolly Nyame.

Dubban magoya bayan APC daga fadin kananan hukumomi 16 da ke jihar sun halarci taron kamfen din.

Mutane 2 sun mutu a wajen gangamin kamfen din Buhari a Jalingo

Mutane 2 sun mutu a wajen gangamin kamfen din Buhari a Jalingo
Source: UGC

An tattaro cewa anyi gaggawan kai wadanda abun ya cika dasu cikin motocin asibiti da aka ajiye a wajen taron.

Hakazalika yawan jama’a ya dakatar da zirga-zirgan motoci na tsawon wasu sa’o’i a hanyar Jalingo-Yola.

Shugaban kasa Buhari dai na neman zarcew ne a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Daga yanzu za a dunga ba jamian soji kula irin wacca ake ba manyan mutane a filin jirgi – Ministan sufurin sama

A baya mun ji cewa wasu mutane da ake zargin yan iska ne daga jam’iyyar adawa sun lalata manyan hotunan kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na jam’iyyarsa a jihar Taraba gabannin ziyarar da Shugaban kasar ke shirin kaiwa Jalingo, babbar birnin jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa wani majiya daga jamiyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyna cewa Shugaban kasar ya bukaci mambobin APC a jihar da kada su rama samma su ci gaba da gudanar da harkokin kamfen dinsu cikin kwanciyar hankali da lumana.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel