Ana kishin-kishin din cewa an hana El-Rufai zuwa Amurka

Ana kishin-kishin din cewa an hana El-Rufai zuwa Amurka

- Ana kishin kishin cewa ana neman El-Rufai a kasar Amurka

- Sahara Reporters tace Jami’an Amurka na neman El-Rufai

- Kwanan nan ne kuma Malam El-Rufai yayi wata barambarama

Ana kishin-kishin din cewa an hana El-Rufai zuwa Amurka

Tun 2010 Jami’an Amurka su ka sa wa El-Rufai takunkumi
Source: Depositphotos

Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce bayan wasu kalamai da gwamnan jihar Kaduna watau Malam Nasir El-Rufai yayi, an kuma fara rade-radin cewa an hana sa shiga cikin kasar Amurka saboda wasu laifuffuka da ake zargin sa da aikatawa.

Kwanan nan ne aka ji gwamna Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yana barazana ga mutanen kasar wajen da ke shirin shigowa Najeriya domin aikin zaben 2019. Gwamnan yace sam ba za su yarda da wani katsalandan ba.

Kamar yadda ku ka sani, gwamnan na jam’iyyar APC mai mulki yace duk wanda yayi kokarin yi wa zaben na Najeriya shiga shara babu shanu, za a maida gawar sa zuwa kasar da ya fito. Daga baya dai dole gwamnan yayi karin haske.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya fadi zaben 2019 ya gama tun yanzu inji jigon PDP

Jaridar Sahara Reporters tace an haramtawa gwamnan shiga cikin Amurka tun shekaru kusan 10 da su ka wuce. Majiyar tace ana zargin tsohon ministan kasar nan ne da aikata wasu almudahana a lokacin yana cikin gwamnatin PDP.

Sahara Reporters ta rahoto cewa rabon Nasir El-Rufai da iya shiga Amurka tun 2010 inda jami’an kasar ke neman sa ido rufe. Sai dai ba a bada wasu hujjoji da karin bayani game da wannan zargi wanda gwamnan dai bai musanya ba.

A kwanakin bayan nan an yi ta zargin ‘dan takarar PDP cewa ana neman sa ruwa a jallo a Amurka wanda daga baya ya shiga kasar. Malam El-Rufai dai ya taba zama a Amurka lokacin da Najeriya tayi masa zafi lokacin shugaba ‘Yar’adua.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel