Yanzu-yanzu: INEC ta saki samfurin takardan kuri'a dauke da jam'iyyu 91

Yanzu-yanzu: INEC ta saki samfurin takardan kuri'a dauke da jam'iyyu 91

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta bayyana hoton samfurin takardan kada kuri'a a zaben shugaban kasan Najeriya da za'a gudanar ranan 16 ga watan Febrairu, 2018 a fadin tarayya.

Takardan kada kuri'ar wannan karo zai dauki jam'iyyun siyasa 91 da hoton tambarin kowace jam'iyya. Saboda rashin isasshen wuri, za'a sanya hotunan yan takaran a takardan ba.

KU KARANTA: Jihar Taraba ta cika ta banbatse domin Buhari

Yanzu-yanzu: INEC ta saki samfurin takardan kuri'a dauke da jam'iyyu 91

Yanzu-yanzu: INEC ta saki samfurin takardan kuri'a dauke da jam'iyyu 91
Source: Facebook

A bangare guda, mun samu labari cewa wasu sun fara kira a dakatar da ‘dan takarar jam'iyyar PDP na shugaban kasa a zaben 2019 watau Alhaji Atiku Abubakar daga takara inda ake zargin cewa ba a Najeriya aka haife sa ba.

Dr. Bunmi Awoyemi yayi wani rubutu a cikin makon nan inda yake cewa Atiku Abubakar ba haifaffen ‘Dan Najeriya bane. Marubucin yace an haifi Atiku ne a wani karamin gari ne da ake kira Jada wanda a da yankin na cikin kasar Kamaru.

Sai bayan an haifi Atiku Abubakar da dadewa ne sannan yankin Jada da kewaye na Arewacin kasar Kamaru su ka shigo cikin Najeriya. Wannan ya sa wasu ke ganin cewa dokar kasar nan ta haramtawa Atiku tsayawa takara a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel