Antoni Janar Malami ya shigar da sabbin kararraki kan Onnoghen a kotun Masana'antu

Antoni Janar Malami ya shigar da sabbin kararraki kan Onnoghen a kotun Masana'antu

- Ofishin Attorney janar na tarayyar Najeriya ya mika kara ga kotun ma'aikatar shari'a

- Yana kalubalantar shari'ar dakataccen alkalin alkalai

- Rashin bayyanar lauyoyi gaban kotu yasa aka dage shari'ar zuwa 14 ga watan Maris

Antoni Janar Malami ya shigar da sabbin kararraki kan Onnoghen a kotun Masana'antu

Antoni Janar Malami ya shigar da sabbin kararraki kan Onnoghen a kotun Masana'antu
Source: Depositphotos

Ofishin Attorney janar na tarayyar Najeriya ya mika kara hudu ga kotun ma'aikatu ta kasa a Abuja, yana kalubalantar gurfanar da mai shari'a Walter Onnoghen a kotun manyan laifuka.

Peter Abang, mai kara wanda shima lauya ne, ya mika karar ne don kalubalantar shari'ar CCT akan dakataccen alkalin alkalai na Najeriya.

A komawa sauraron shari'ar a ranar alhamis, Lauyan mai kara, James Igwe ya sanar da kotun cewa mai kara na farko, a ranar laraba ya bashi dalilan hudu.

Igwe, yace ya maida martani ga kararrakin kuma a shirye yake da ya cigaba.

GA WANNAN: Mun nemi, sama ko kasa, tsohon shugaban NIA mun rasa, baya gida shi da matarsa - EFCC

Lauyoyin sauran basu zo kotun ba sai lauyan AGF, Dauda Lamiri, wanda ya sanar da kotun cewa an sanar da wadanda ake kara.

Igwe ya kara da cewa sauran lauyoyin basu bada dalilin rashin bayyanar su a kotu ba.

A don haka ne ya bukaci dage sauraron shari'ar. Yace za a iya duba duk sauran bukatun a ranar da za a dawo kotu sai a fara da kalubalen shari'ar.

Igwe yace hakan zai ba kotun damar yin shari'ar a natse.

Mai shari'a Sanusi Kado ya dage sauraron shari'ar zuwa 14 ga watan maris.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel