Daga yanzu za a dunga ba jamian soji kula irin wacca ake ba manyan mutane a filin jirgi – Ministan sufurin sama

Daga yanzu za a dunga ba jamian soji kula irin wacca ake ba manyan mutane a filin jirgi – Ministan sufurin sama

Rahotanni da ke zuwa mana ya nuna cewa daga yanzu za a dunga ba jami’an sojoji kula na mussamman da alfarma irin wanda ake ba manyan mutane masu muhimmanci a lokacin duba masu hawa jirgi a kowani filin jirgin sama da ke Najeriya.

Sanata Hadi Sirika, ministan sufurin sama ya bayyana hakan a ranar Laraba, 6 ga watan Fabrairu.

James Odaudu, kakakin ministan wanda ya wakilci ministan a lokacin wata ziyara da mambobi daga hedkwatar tsaro suika kawo ne ya bayar da wannan umurnin.

Daga yanzu za a dunga ba jamian soji kula irin wacca ake ba manyan mutane a filin jirgi – Ministan sufurin sama

Daga yanzu za a dunga ba jamian soji kula irin wacca ake ba manyan mutane a filin jirgi – Ministan sufurin sama
Source: Depositphotos

Don haka, Sirika ya bayar da umurni ga hukumar kula da filayen jirgin sama na Najeriya (NAF) da kuma sauran hukumomi da ke hukumar domin suyi gaggawan sanya shi cikin manufofi da ayyuka don nuna godiya fa jami’an soi masu ritaya a Najerita kamar yadda ake yi a sauran kasashen da suka ci gaba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnati ta koka da yadda Iyaye ke yi wa 'Ya 'yan su ciki a Jihar Edo kamar hauka

Sirika ya kuma yi umurnin cewa a kara sakonni da ke nuna godiya ga sadaukarwa da nasarorin sojoji cikin sanarwar da ake na tsarar da ke tsakanin tashi da saukar jirage.

Ministan ya kuma yi alkawarin yin hotuna da izinin hukumomin sojojin, don nuna godiya ga jajircewa da sadaukarwar hukumomin sojin Najeriya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel