Kudin Ikoyi: Daga karshe kotu ta bayar da izinin kama tsohon Shugaban NIA da matarsa

Kudin Ikoyi: Daga karshe kotu ta bayar da izinin kama tsohon Shugaban NIA da matarsa

- Kotu ta bayar da izini don kama tsohon Shugaban hukumar leken asiri na kasa, Ambasada Ayodele Oke da uwargidarsa, Folashade

- Hakan na da alaka da $43,449,947, £27,800 da kuma N23,218,000 da aka gano a wani katafaren gida a Ikoyi

- Hukumar EFCC ce ta nemi izinin kama Oke da matarsa

Wata kotu ta bayar da izini don kama tsohon Shugaban hukumar leken asiri na kasa, Ambasada Ayodele Oke da uwargidarsa, Folashade.

A cewar NAN, izinin kamun na da nasaba da $43,449,947, £27,800 da kuma N23,218,000 da aka gano a wani katafaren gida a Ikoyi.

Kudin Ikoyi: Daga karshe kotu ta bayar da izinin kama tsohon Shugaban NIA da matarsa

Kudin Ikoyi: Daga karshe kotu ta bayar da izinin kama tsohon Shugaban NIA da matarsa
Source: Depositphotos

Ku tuna cewa Legit.ng ta ruwaito a baya cewa hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta bayyana cewa tana neman izinin kama Oke da matarsa.

Sai dai kuma ba a yi nasarar gurfanar da su ba kuma saboda EFCC bata riga da ta snya tuhume-tuhume akan su biyun ba.

KU KARANTA KUMA: Mambobin PDP sun koma APC a Akwa Ibom

Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo a ranar Laraba, 6 ga watan Fabrairu ya sanar da Justis Chukwujekwu Aneke cewa yana da kudirin neman wani izini na baki, wanda zai ba su izinin kama dakataccen Shugaban hukumar leken asiri na kasa da matarsa.

Hakan ya kasance ne saboda hukumar na fuskantar matsala wajen bayyanar wadanda ake karan su biyu a gaban kotu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel