Ma'aikatan jihar Adamawa sun zargi Bindow da kamfe da kudaden albashinsu

Ma'aikatan jihar Adamawa sun zargi Bindow da kamfe da kudaden albashinsu

- Ma'aikatan jihar Adamawa na zargin gwamna Mohammed Bindow da laifin zaftare sama da miliyan 300 daga albashin su na watan Janairu saboda dalilin da suka kwatanta da siyasa

- Wasu daga cikin ma'aikatan sunyi magana da majiyar mu, sunce an zaftarar musu albashi babu sanarwa daga kungiyar kwadago ko wajen aiyukan su

Ma'aikatan jihar Adamawa sun zargi Bindow da kamfe da kudaden albashinsu

Ma'aikatan jihar Adamawa sun zargi Bindow da kamfe da kudaden albashinsu
Source: Depositphotos

Kamar yanda suka ce, bincike ya bayyana cewa an zaftare kudaden ne don yawon kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kudin sunce za'ayi amfani dasu ne don hayar mutane da zasu nuna cewa shugaban kasar na da magoya baya a jihar.

Wata darakta tace: Bayan binciken da nayi daga ma'aikatar kudi, na gano cewa an zaftare albashin mu ne don kamfen din shugaban kasa a Yola a ranar alhamis.

GA WANNAN: Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

Abin yayi mana ciwo ace tun 2015 gwamna Bindow yaki biyan mu kudin hutun mu, yanzu kuma dan albashin namu ne ya kwashe don hayar mutane. A saboda hakan ne APC ta rasa goyon bayan ma'aikatan jihar Adamawa.

Ma'aikatan sun tabbatar da cewa idan shuwagabannin kwadago suka ki karbar musu kudin su daga gwamnati, zasu tafi yajin aiki.

Lokacin da majiyar mu ta samu shugaban kungiyar kwadago na jihar Adamawa, Mr Jeremiah Ngyakwar, ya tabbatar da cewa ya samu korafe korafe akan rage albashi kuma yayi magana da ofishin babban akawun jihar, amma har yanzu bai bada amsa akan matsalar ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel