2019: Atiku baya iya cin jihar Ogun - Masana

2019: Atiku baya iya cin jihar Ogun - Masana

- Babu yuwuwar samun kuri'u ga Atiku a jihar Ogun

- Har yanzu shine yafi kowa suna kuma da karbuwa a jihar

- Cigaba da mulkin shi zai kawo cigaba ga ga matasa da kasar baki daya

2019: Atiku baya iya cin jihar Ogun - Masana

2019: Atiku baya iya cin jihar Ogun - Masana
Source: Facebook

Mashiryin kungiyar kamfen din matasa ta Buhari reshen jihar Ogun, Olusegun Clement, a ranar alhamis yace babu yuwuwar Dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar yayi nasarar zaben 16 ga watan Fabrairu a jihar.

Clement ya sanar da hakan ne yayi rantsar da yan kungiyar a Abeukuta.

Yace yanda aka san shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma karbuwar shi a jihar ne ya nuna cewa babu dan takarar da zai yi nasarar lashe jihar banda shi.

Shugaban ya kwatanta Atiku da cewa ba wani barazana bane ga komawar Buhari kujerar shi, kari da ganin cewa shugaban kasar ya gyara kasar a mulkin shi farko don haka ya cancanci komawa kujerar shi.

Clement, tsohon mataimaki na musamman ga gwamna Ibikunle Amosun akan lamurran dalibai, yace da sake zabar Buhari a zabe mai zuwa, matasa ma zasu ji dadi.

"Mu dai a Ogun, abinda mukeyi shine wayar da kai da kuma jawo mutane saboda babu dan takarar da yayi suna kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari."

GA WANNAN: Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

"Wannna na nuna farin aiyukan mu a Ogun kuma zamu cigaba har sai saura awa 48 zuwa zaben shugaban kasa. Zamu ziyarci lungu da sako na jihar, tare da kai sakon shugaban kasar garesu," inji shi.

Clement ya hori matasa dasu guji duk wata tashin tashina tare da kai rahoton duk wanda zai yi amfani dasu wajen karya doka.

Clement ya kuma roke su dasuyi zabe na hankali, cewa da Buhari ne kadai ya cancanta kuma zai cigaba da kawo romon damokaradiyya ga yan Najeriya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel