Goyon bayan Atiku babu abunda zai canja a sakamakon zaben Shugaban kasa – Kungiyar Arewa

Goyon bayan Atiku babu abunda zai canja a sakamakon zaben Shugaban kasa – Kungiyar Arewa

Babban sakataren kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Cif Anthony Sani ya ayyana goyon bayn da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ke ta samu a ranar Lahadi da ya gabata a matsayin wani shiri da ba zai shafi sakamakon zaben Shugaban kasa ba ko kadan.

Sani yace goyon bayan Atiku da kungiyoyin Afenifere, Ohanaeze, Pan-Niger, Middle Belt Forum da na dattawan Arewa suka yi duk ba wani sabon abu bane, cewa dukkanin kungiyoyin baya ga na dattawan Arewa duk sun marawa dan takarar Shugaban kasa na PDP baya a zaben 2015.

A cewarsa: “Menene sabon abu a wannan goyon bayan zancen gaskiya shine hakan ba zai shafi sakamakon zabe ba, saboda wadannan kungiyoyi ba su isa wakiltan dukkanin mutanen yankinsu ba.

“Muna ganin bai kamata a ta yin wani sharhi akai ba saboda ba sabon abu bane.

Goyon bayan Atiku babu abunda zai canja a sakamakon zaben Shugaban kasa – Kungiyar Arewa

Goyon bayan Atiku babu abunda zai canja a sakamakon zaben Shugaban kasa – Kungiyar Arewa
Source: UGC

“Goyon bayan ba wani sabon abu bane saboda baya ga kungiyar dattawan arewa da Farfesa Ango Abdullahi ke shugabanta, dukkanin sauran kungiyoin da suka mara masa baya sun yi aiki tare da PDP a 2015 amma duk da hakan APC ce tayi nasara.

“Saboda haka wannan ba zai wani shafi sakamakon zaben 2019 ba saboda wadannan kungiyoyi ba su isa su ci ma dukkanin yankin da suke wakilta albasa ba.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya baiwa jahar Zamfara N60,000,000,000 a matsayin biyan bashi

“Da fatan za ku san cewa ACF wacce kungiya c eta Arewa, ba ra’ayinta daya da gamayyar kungiyar arewa wanda farfesa Ango Abdullahi ke wakilta ba.

“Goyon bayan shugaba Buhari da manyan Janar 71 suka yi ya kori jita-jitan cewa tsoffin janar sun hada kai domin tsige Buhari.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel