Masu aikin N-Power za su zabi Shugaba Buhari ya zarce a mulki

Masu aikin N-Power za su zabi Shugaba Buhari ya zarce a mulki

Mun ji labari cewa da-dama na wadanda su ka samu shiga cikin tsarin nan na N-Power da gwamnatin tarayya ta shugaba Buhari ta kawo, za su zabi jam’iyyar APC mai mulki a 2019 domin shirin ya dore.

Masu aikin N-Power za su zabi Shugaba Buhari ya zarce a mulki

Da dama na masu aikin N-Power za su yi Buhari a zaben 2019
Source: UGC

A cikin makon nan ne wasu daga cikin wadanda su ka samu wannan aiki na N-Power su ka cika hanyoyin cikin Garin Abuja inda su ke nuna goyon bayan su ga shugaba Buhari inda su kace sun yi na’am da tazarcen wannan gwamnatin.

Wasu daga cikin ma’aikatan na N-Power wadanda su ka nuna na’am din su da gwamnatin APC sun yi hira da ‘yan jarida jiya a Abuja inda su ka bayyana cewa sun fitar da matsaya cewa lallai za su zabi Muhammadu Buhari ne a zaben bana.

KU KARANTA: Osinbajo ya bada umurnin bude shafin daukan aikin N-Power

Wani Bawan Allah mai suna Abdulwasiu Akanbi, ya fadawa manema labari cewa gwamnatin Buhari tayi namijin kokari wajen samawa Matasa aikin yi a Najeriya, wanda a da su ke gara-ramba a gari su na neman hanyar cin abinci.

Abdulwasiu Akanbi yace da shi da wasun su, za su dangwalawa shugaba Buhari ne a zaben 16 ga wannan wata da zayi. Akanbi ya bayyana cewa sama da Matasa 500, 000 gwamnatin APC ta dauka aiki ta shirin na N-Power da ta kawo.

Malamai ma dai sun yaba da wannan tsari na gwamnatin Buhari inda su kace sun ga banbanci a makarantun su. Gwamnatin tarayya ta na biyan Matasa N30, 000 kowane wata domin cike gibin da ake da shi na kwararrun Malamai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel