Zabe: Matsayar fadar shugaban kasa a kan gargadin da El-Rufai ya yiwa kasashen waje

Zabe: Matsayar fadar shugaban kasa a kan gargadin da El-Rufai ya yiwa kasashen waje

- Fadar Shugaban kasa ta ce ta gamsu da karin bayanin da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi a akan batun hana kasashen waje yin katsalandan a zaben Najeriya

- Fadar shugaban kasar tayi alkawarin gudanar da sahihiyar zabe amma ta ce ba za ta amince da wasu kasashe masu niyyar yin katsalandan a zaben ba

- Gwamna Nasir El-Rufai ya ce ba fitina ya ke neman tayarwa ba sai dai ya yi gargadin ne domin kare mutunci da 'yancin Najeriya a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta

Fadar shugban kasar Najeriya ta yi tofa albarkacin bakin ta a kan gargadin da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi a kan kasashen waje da ke neman yin katsalandan a babban zaben Najeriya da ke tafe.

El-Rufai ya ce Najeriya ba za ta amince da duk wani irin katsalandan ko kutse daga wata kasar waje ba yayin gudanar da babban zaben.

Ya yi wannan jawabin ne a wani shirin Tuesday Live da aka watsa a gidan talabijin na kasa NTA.

"Wasu na kiran kasashen waje su zo su saka baki a zaben Najeriya, muna jiran zuwansu. Za su koma kasashensu a cikin jakunkunan gawa domin babu wanda zai zo ya koya mana yadda zamu tafiyar da kasarmu," inji shi.

Zabe: Matsayar fadar shugaban kasa a kan gargadin da El-Rufai ya yiwa kasashen waje

Zabe: Matsayar fadar shugaban kasa a kan gargadin da El-Rufai ya yiwa kasashen waje
Source: UGC

DUBA WANNAN: Abinda na fadawa sarakunan Nasarawa yayin ganawar sirri da mu kayi - Buhari

Wasu da dama sun ce El-Rufai yana neman tayar da rikici ne sai dai ya yi karin haske inda ya ce yana kare kima da darajar Najeriya ne a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta.

Fadar Shugaban kasar ta ce ta gamsu da bayyanan da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi a kan batun kamar yadda ya ke cikin wani sakon e-mail da ta aike wa Premium Times.

A cikin sakon, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce fadar shugaban kasa a karkashin mulkin Shugaba Buhari za ta bawa masu sanya idanu a kan zabe hadin kai amma ba zata amince da kasashen waje da ke neman yin katsalandan a zaben ba.

"Fadar shugaban kasar ta tabbatarwa 'yan Najeriya da kasashen waje cewa za tayi duk mai yiwuwa domin ganin ta gudanar da sahihiyar zabe mai tsafta kuma cikin zaman lafiya.

"Mun ga karin bayanin da Gwamna jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi a kan kalaman da ya furta a baya a kan kasashen da ke kokarin yin katsalandan a zaben Najeriya kuma muna fatan karin bayanin da ya yi zai gamsar da kowa," inji Fadar shugaban kasar.

Sakon ya kuma ce "Gwamnan ya yi magana ne domin kare kima da darajar Najeriya. Babu tantama El-Rufai da jam'iyyar mu ta APC sun dogara ne da demokradiyya ta hanyar gudanr da zabe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel