Kungiyar I Believe in President Muhammadu Buhari 2019 tace APC za ta kawo Kasar Ibo

Kungiyar I Believe in President Muhammadu Buhari 2019 tace APC za ta kawo Kasar Ibo

Shugaban wata kungiya mai rajin ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce a kan mulki a zaben 2019 ya sha alwashin hana ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar samun nasara a kudu maso gabas.

Kungiyar "I Believe in President Muhammadu Buhari 2019 tace APC za ta kawo Kasar Ibo"

Shugaban "I Believe in President Muhammadu Buhari yace APC za ta doke PDP
Source: Twitter

Mista Frank Ezike wanda shi ne shugaban kungiyar “I Believe in President Muhammadu Buhari 2019,” ya bayyana cewa ba za su bari Atiku Abubakar ya doke shugaba Buhari a zaben da za ayi a cikin wannan watan na Fubrairu ba.

Frank Ezike ya maida martani ne ga mubaya’ar da aka ji babbar kungiyar nan ta kasar Ibo watau Ohanaeze Ndigbo, tayi wa Atiku Abubakar na PDP. Ezike yace kungiyar su ba za ta bari Inyamurai su zabi Alhaji Atiku Abubakar ba.

KU KARANTA: Buhari ya fadi zaben 2019 ya gama inji Jigon PDP a Anambra

Mista Ezike ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya aikawa jaridar Punch jiya yana mai cewa za su hada kan mutanen kasar Ibo domin ganin sun zabi shugaba Buhari a wannan karo. Ezike yace yin hakan ne zai ceci yankin a kasar.

Ezike yace Buhari ne zai lashe zabe a jihohin yankin na kudu maso gabas a zaben bana. Hakan dai akasin abin da kungiyar Ohanaeze Ndigbo tayi alkawari ne inda ta ke sa ran a zabi PDP daga sama har kasa a zaben da za ayi kwanan nan.

A cikin tafiyar ta Ohanaze, kwanaki kun ji cewa Sakataren kungiyar watau Uche Okwukwu, shi ma yayi kira ga jama’a su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC a zaben shekarar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel