Shugaba Buhari ya baiwa jahar Zamfara N60,000,000,000 a matsayin biyan bashi

Shugaba Buhari ya baiwa jahar Zamfara N60,000,000,000 a matsayin biyan bashi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya biya jahar Zamfara kimanin naira biliyan sittin, N60,000,000,000 a matsayin biyan bashin kudaden da ta kashe wajen kula da manyan hanyoyin hanyar gwamnatin tarayya dake jahar.

Gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari ne ya tabbatar da haka a yayin yakin neman zaben daya gudanar a garin a karamar hukumar Shinkafi, inda yace zasu yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka kamata don amfanin jama’an jahar gaba daya.

KU KARANTA: Ganduje ya bude ma Atiku dandanlin da zai gudanar da gangamin yakin neman zabe

Sai dai Gwamna Yari bai bayyana adadin kudin ba, amma tun a watan Agusta na shekarar 2018 ne majalisar dattijai ta Najeriya ta amince ma shugaban kasa Muhammadu Buhari daya biya jahar Zamfara bashin da take bi na naira biliyan sittin da miliyan biyu.

A jimlace, majalisar ta amince ma Buhari ya biya jihohin Najeriya guda ashirin da daya, 21, bashin kudaden da suka binta da suka kashe wajen ginawa tare da kula da hanyoyin gwamnatin tarayya dake jihgohinsu, kudin daya kai naira biliyan 489.

A jawabinsa, Gwamna Yari yace tuni shugaba Buhari ya sanya hannu akan amincewa a biya jahar Zamfara kudinta, “Ina tabbatar muku idan har gwamnati ta biyamu kudinnan, za ayi muku aiki dasu koda bayan saukana daga mulki.

“Ina da tabbacin dan takararmu na jam’iyyar APC, Mukhtar Shehu Idris zai kashe kudin ta hanyoyi da suka dace, ba zai bamu kunya ba, kuma zai cigaba da kyawawan ayyukan da muka fara, ina kira gareku daku zabeshi a matsayin gwamnanmu na gobe, tare da Ahmad Gumi a matsayin mataimakinsa.” Inji shi.

Daga karshe Yari ya tabbatar ma jama’an Shinkafi cewa ya cika duk alkawurran daya daukan musu a a yayin yakin neman zabe na shekarar 2015, tun daga abinda ya shafi kiwon lafiya, hanyoyi, ilimi, tallafi da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel