Tun kafin a kai ko ina: Shugaba Buhari ya fadi zabe ya gama inji Obaze

Tun kafin a kai ko ina: Shugaba Buhari ya fadi zabe ya gama inji Obaze

Shugaban yakin neman zaben Atiku Abubakar da kuma Peter Obi na PDP a zaben 2019 a jihar Anambra, Oseloka Obaze, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya riga ya fadi zaben 2019 da za ayi.

Tun kafin a kai ko ina: Shugaba Buhari ya fadi zabe ya gama inji Obaze

Obaze yace tun kafin a kai ko ina Buhari ya fadi zaben bana
Source: Twitter

A Ranar Laraban nan ne Mista Oseloka Obaze ya fito ya bayyana cewa za ayi waje da gwamnatin shugaba Buhari a zaben da za ayi a Ranar 16 ga watan Fubrairu. Obaze yace yanzu jira kurum ake yi Atiku ya zama shugaban kasa.

Obaze wanda yayi takarar gwamnan jihar Anambra a zaben 2017, ya bayyana cewa fiye da kashi 90% na mutanen Najeriya sun gaji da gwamnatin nan mai-ci ta shugaba Buhari don haka za su zabi ‘dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Buhari zai kirkiro wata sabuwar Jiha a cikin Kudancin Najeriya – inji Gwamnan Anambra

Tsohon ‘dan takarar gwamnan yace jam’iyyar APC ba ta cika akalla kashi 5% rak na alkawuran da tayi wa mutanen Najeriya a lokacin yakin neman zabe ba. Wannan ya sa akasarin jama’a ke jiran lokacin zabe su zabi PDP inji Obaze.

Obaze ya na mai bada tabbacin cewa Buhari ba zai zarce a kan mulki ba inda ya kuma kara da cewa jam’iyyar su ta PDP tayi duk wani shiri na ganin cewa ba a murde zaben na bana ba. Obaze yace Turawa za su zura ido a zaben na 2019.

Oseloka Obaze wanda shi ne shugaban yakin zaben PDP a 2019 a jihar ta Anambra ya musanya cewa gwamnonin Kudu maso gabashin Najeriya ba su tare da Atiku Abubakar da Peter Obi 100 bisa 100.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel