Mun nemi, sama ko kasa, tsohon shugaban NIA mun rasa, baya gida shi da matarsa - EFCC

Mun nemi, sama ko kasa, tsohon shugaban NIA mun rasa, baya gida shi da matarsa - EFCC

- Hukumar yaki da rashawa tace bata samu Oke da matar shi a gidansu ba

- Ana zargin ya tsere ya bar kasar kafin ranar da zai gurfana gaban kuliya

- Alkalin mai shari'a yace ba a gabatar da karar yanda yakamata ba

Mun nemi, sama ko kasa, tsohon shugaban NIA mun rasa, baya gida shi da matarsa - EFCC

Mun nemi, sama ko kasa, tsohon shugaban NIA mun rasa, baya gida shi da matarsa - EFCC
Source: Depositphotos

Hukumar yaki da rashawa tace ba a samu Oke da matar shi a sanannen adireshin su ba.

Tsohon darakta janar din NIA, Ambasada Ayodele Oke da Matarshi, Folashade har yanzu ba a basu takardar tuhumar su da ake da almundahanar kudude ba.

Ana zargin su biyun suna da hadi da dala 43,449,947,000 da aka samu a flat 7B, lamba 16 a titin Osborne, Ikoyi Legas.

Hukumar yaki da rashawan ta sanar da babban kotun tarayya ta Legas cewa har yanzu bata basu takardar ba saboda ba a same su a gidan su ba.

Lauyan masu kara Rotimi Oyedepo yace: "Muna samun matsala ta wurin kai musu sammacin. Munje gidan su amma basa nan balle mu basu."

Kamar yanda yace, ACJA ta bada damar mai shari'a ya bada umarnin yanda za a kira wandanda ake zargin zuwa kotu. Mai shari'a Aneke yaki bada umarnin, yace ba a kawo shari'ar ta yanda ya dace ba.

GA WANNAN: An yanke wa shugaban kungiyar direbobi hukuncin rataya, shekaru takwas bayan ya kashe dansanda

Yace: "Banga takardun ku ba, sai na gansu ne zansan irin gaggawar da ake so don su bayyana. Bazan bada umarni ba bayan bansan kuma anyi kokarin ku ba."

Mun ruwaito cewa Ayodele Oke, tsohon daraktan NIA da matarshi sun tsere sun bar kasar bayan kwanaki kadan ne suka rage hukumar yaki da rashawa su gurfanar dasu a gaban kuliya.

Oke da matarshi yakamata su fuskanci kotu akan zargin rashawa daga hukumar yaki da rashawa a ranar juma'a daya ga watan Fabrairu.

An gano cewa ya tsere ya bar kasar zuwa turai don dalilin rashin lafiya.

Shari'ar rashawar akan kudi dala miliyan arba'in, pam 27,000 da Naira miliyan 23 daga wani gida a Ikoyi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel