Buhari ko Atiku daya daga cikinsu ne zai kafa gwamna a jihar Filato

Buhari ko Atiku daya daga cikinsu ne zai kafa gwamna a jihar Filato

- Shin mene ne makomar jihar Filato a zabubbuka masu zuwa

- Dama jiha ce da shugaban kasa Mammadu Buhari bai taba ci ba a zabukan baya

- Sanata Jang yayi alkawarin kai kuri'u miliyan biyu daga jihar Filato

Buhari ko Atiku daya daga cikinsu ne zai kafa gwamna a jihar Filato

Buhari ko Atiku daya daga cikinsu ne zai kafa gwamna a jihar Filato
Source: UGC

A mutane wadanda sukayi rijistar katin zabe 2,480,455 na jihar Filato, ko mutane nawa jam'iyyar APC da kuma PDP zata gamsar dasu don kada mata kuri'a?

Akwai rashin tabbaci akan makomar PDP a jihar da ta mulka na tsawon shekaru 16 inda sai a 2015 da APC ta karbe mulkin.

A cikin kasa da kwanaki 10 da suka rage na zaben shugabancin kasa kuma da katikan zabe 201,049 da ba a karba ba a jihar, APC da PDP na da burin cafkar jihar mai arzikiin noman dankalin turawa.

Duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba cin jihar ba, amma jam'iyyar shi na fatan cin fiye da kashi 40 cikin dari da tayi a zabukan 2015.

A cikin mutane 1,076,833 da aka amince zasuyi zabe a 2015 a jihar, PDP ta wuce APC da kadan ne inda tasa Jonathan ya samu kuri'u 549,615 sama da Buhari mai 429,140.

PDP ce ke gaba a Langtang ta kudi, Langtang ta arewa, Riyom, Kanke, Jos ta kudu, Barkin Ladi, Bassa, Bokkos, Pankshin, Mikang, Mangu da Qua'a Pan inda APC ta ke ja gaba a Jos ta arewa, Shendam, Kanam, Jos ta gabas da Wase.

GA WANNAN: Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

Ba dole hakan ya canza ba sai dai PDP bata jin dadin jam'iyyar mai mulki a matakin tarayya da jihohi. Sai dai kuma anyi kintacen cewa chanza shekar jiga jigan yan PDP irin su Sen. Victor Lar, Chris Giwa, Sen sati Gogwim, Auwalu shehu maihula, Shehu Saleh Hassan, Ayuba Burku Gufwan da sauran su kan iya janye kuri'un PDP daga Langtang ta arewa, Mangu da Jos ta kudu.

Amma kuma PDP zatayi amfani da kabilanci da addini hade da kashe kashen Berom da Fulani a jihar, don samar da goyon baya ga dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar ta.

Rinjayen Sen. Jang a cikin mutanen shi na Berom kamar yanda yace zai kawo wa PDP kuri'u miliyan biyu abin dubawa ne.

Duk da mashiryin kamfen din jihar ta bakin jami'in yada labarai yace kuri'u miliyan biyun zasu samu ne matukar dukkan mutanen jihar suka fito don yin zabe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel