Yajin aikin da Malaman Jami’o’i su ke yi bini-bini bai dace ba – Saraki

Yajin aikin da Malaman Jami’o’i su ke yi bini-bini bai dace ba – Saraki

Mun samu labari cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, AbubakarBukola Saraki, yayi kira ga gwamnatin tarayya tayi kokarin ganin an kawo karshen yajin aikin da ake yi a jami’o’in kasar nan.

Yajin aikin da Malaman Jami’o’i su ke yi bini-bini bai dace ba – Saraki

Bukola Saraki yana so a daina tafiya yajin aiki a Jami’o’i
Source: Depositphotos

Kamar yadda mu ka samu labari a cikin tsakiyar makon nan, Saraki yayi wannan kira ne a jiya Laraba ta bakin mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai watau Yusuph Olaniyonu. Yanzu dai an shafe watanni 3 ana ta yajin aiki.

A jawabin da shugaban majalisar ya fitar ta hannun hadimin sa, Yusuph Olaniyonu, Saraki ya nemi a bude makarantun jami’o’in cikin gaggawa. Bukola Saraki yake cewa yajin aikin yana da mummunan tasiri a kan matasan kasar.

KU KARANTA: Yajin aiki: Gwamnati da Malamai za su yi zama na karshe yau

Bukola Saraki yana mai cewa akwai ‘daliban da su kayi rajistar zabe a cikin makarantun su, don haka idan aka cigaba da yajin aiki, za su rasa yin zabe a bana. Tun farkon watan Nuwamban bara ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki.

Matasan Najeriya sun haura kashi 50% na masu zabe a Najeriya don haka Saraki yace ba zai yiwu a rufe jami’o’i ba kuma a zura idanu ayi zuru. Shugaban majalisar kasar yace dole a kawo karshen yajin aikin da ake yawan yi a Najeriya.

A karshen dai Sanatan ya nemi gwamnatin tarayya ta biyawa malaman jami’o’i bukatun su tare da cika duk alkawuran da aka dauka a baya. Saraki yace majalisar tarayya za ta cigaba da kokarin ganin an inganta harkar ilmi a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel