Gabanin zabe: Wasu matasa sun farfasa allunan yakin neman zaben Buhari a Maiduguri

Gabanin zabe: Wasu matasa sun farfasa allunan yakin neman zaben Buhari a Maiduguri

Wasu hotuna da suka rika yawo a kafafen sadarwar zamani sun yi nuni ne da yadda wasu matasa suka farfasa tare da lalata allunan yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari da sauran 'yan takarkari a jam'iyyar APC mai mulki a jihar Borno.

Hotunan dai wadanda aka ce an kafa su ne a cikin kokuwar garin Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno ance mafusatan matasan sun yi ta bin su daya-bayan-daya suna fasawa, lamarin da bai yi wa magoya bayan na APC dadi ba.

Gabanin zabe: Wasu matasa sun farfasa allunan yakin neman zaben Buhari a Maiduguri

Gabanin zabe: Wasu matasa sun farfasa allunan yakin neman zaben Buhari a Maiduguri
Source: UGC

KU KARANTA: Dakin kwanan dalibai mata ya kone a jami'ar Kano

Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan ta'asar dai na zuwa ne awanni kadan bayan da dan takarar shugabancin kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci garin na Maiduri.

A wani labarin kuma, Tsaffin ma'aikatan kamfanin jiragen saman Najeriya na Nigeria Airways da suka yi ritaya shekaru da dama da suka shude sun bayyana aniyar su ta zubawa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ruwan kuri'un su a zaben da ke tafe.

Tsaffin ma'aikatan wadanda yanzu haka suke karbar fansho sun bayyana jin dadin su karara ta yandda suka ce gwamnatocin da suka gabata sun yi fatali da bukatun su na biyan hakkokin su tsawon shekaru 14 amma gwamnatin shugaba Buhari ta share masu kukan su.

Ga dai wasu hotunan nan kamar yadda jaridar Rariya ta wallafa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel