El-Rufai: Gwamnatin APC na yunkurin amfanin da karfin bindiga a zaben 2019 – Sani

El-Rufai: Gwamnatin APC na yunkurin amfanin da karfin bindiga a zaben 2019 – Sani

- El-Rufai yayi barazanar hallaka masu shirin yi wa Najeriya katsalandan a zaben 2019

- Wani Sanatan Jihar Kaduna yace sai an bi a hankali da wannan kalamai na Gwamnan

El-Rufai: Gwamnatin APC na yunkurin amfanin da karfin bindiga a zaben 2019 – Sani

Shehu Sani yayi Allah wadai da kalaman Gwamna El-Rufai
Source: UGC

Mun samu labari jiya cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya maida martani game da barazanar da aka ji gwamnan jihar Kaduna yana yi wa masu neman yin katsalandan a zaben Najeriya.

Sanata Shehu ya bayyana cewa ya kamata Duniya ta bi a hankali da irin wannan kalamai da ke fitowa daga bakin gwamnan na jihar Kaduna. Sanatan yayi wannan jawabi ne a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita.

KU KARANTA: Mataimakin shugaban PDP da matar sa sun mutu a hadarin mota

‘Dan majalisar mai wakiltar yankin tsakiyar Kaduna yayi Allah-wadai da jawabin da gwamnan na jam’iyyare APC mai mulki yayi a lokacin da ya zanta da gidan talabijin na NTA a wani shiri da Cyril Stober ya gudanar a makon nan.

Sanatan yake cewa yayin da jama’a su ke tunanin fita su kada kuri’a, jam’iyyar APC tana neman yadda za ta harbe jama’a ne domin ta murde zaben na bana. Sanatan yake cewa ba akwatin zabe ne ke gaban irin su Nasir El-Rufai ba.

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ma ta maida martani game da wannan kalamai masu ban tsoro inda ta nemi kasashen waje su hana gwamna Malam Nasir El-Rufai barin Najeriya a dalilin haka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel